Tsohon Gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari ya samu gocewar kashi, ya tafi Amurka jinya

Tsohon Gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari ya samu gocewar kashi, ya tafi Amurka jinya

  • Mai neman kujeran shugaba uwar jam'iyyar APC ya shilla Amurka jinyar gocewar kashin da ya samu
  • Shugaban ma'aikatan Abdul Aziz Yari ya bayyana cewa maigidansa ya koma Amurka don sake duba kansa
  • Wannan ya biyo bayan dokar da majalisar wakilai ke kokarin kafawa na haramtawa ma'aikatan gwamnati zuwa kasar waje jinya

Abuja - Tsohon Gwamnan jihar kuma dan takaran kujeran Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC, Alhaji Abdulaziz Yari, ya samu gocewar kashi a kafarsa ta hagu.

Yari ya bayyana hakan ne a sakon raddi ga masu cewa yana cikin matsanancin halin rashin lafiya kuma an garzaya da shi Amurka cikin gaggawa, rahoton Vanguard.

Wani rahoto ya bayyana cewa an kwashe Yari a keke guragu an tafi da shi Ingila.

Gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari
Tsohon Gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari ya samu gocewar kashi, ya tafi Amurka jinya Hoto: Presidency
Asali: UGC

Amma hadimin Yari, Injiniya Abdullahi Abdulkarim Tsafe, ya yi martanin cewa yan adawan Yari ne ke yada labarun karya kan maigidansa.

Yace AbdulAziz Aziz dan Adam ne kaman kowa kuma yana rashin lafiya kaman kowa.

A jawabinsa:

"Ya samu gocewar kashi a kafarsa ta hagu lokacin da yayi tuntube a matakala kuma sakamakon haka ya tafi Amurka jinya; kuma ya dawo makonni biyu da suka gabata kuma yau ya sake koma duba lafiyarsa."
"Saboda haka jama'a da masoyansa suyi watsi da labaran daidaikun mutane."
"Yayinda muke addu'an Allah ya dawo da shi lafiya, zai dawo nan ba da dadewa ba."

Yari na daya daga cikin masu neman kujeran shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC a zaben da za'a yi ranar 26 ga Febrairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel