Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya

Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya

  • Mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya
  • Yan ta'addan da suka mika kansu a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, sun hada da maza 22, mata 27 da kuma yara 55
  • Hedkwatar rundunar sojin ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa Mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa mayakan da suka mika wuya sun hada da maza 22 da mata 27 da yara 55.

Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya
Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa, yan ta’addan da kansu ne suka mika wuya ga dakarun runduna ta musamman ta 25 a yankin Damboa da ke Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ba mu bada sarauta haka kawai: Sarkin Daura yayinda yaiwa Amaechi 'Dan Amanar Daura'

Sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mayakan ISWAP da iyalansu da yawansu ya kai 104 wadanda suka kunshi maza 22, mata 27 da yara 55 sun mika wuya ga runduna ta musamman ta 25 a Damboa, jihar Borno a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairun 2022.”

Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji

A wani labarin, mun kawo a baya cewa a kalla mayakan ISWAP 25 sun nitse a wani kogi mai zurfi a yankin Marte da ke tafkin Chadi a arewa maso gabas yayin da suke tserewa barin wuta da dakarun sojojin Najeriya ke yi ta sama.

Jiragen yakin sojojin, ciki harda Super Tucano na rundunar sojin sama, sun kai mamaya sansanin yan ta'addan a ranakun Laraba da Alhamis a hare-haren da ta shafe tsawon mako tana kaiwa.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta ce ba karatu ranar Litinin a BUK, za a tara dalilai da iyaye a yi musu bayani

Wani jami'in leken asiri da ke yankin ya sanar da PRNigeria cewa jiragen sun yi ta luguden bama-bamai ta sama a sansanoni da ma'ajiyar yan ta'addan na ISWAP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel