Atiku ya ziyarci ‘Yan gudun hijira, ya gwangwaje su da kyautar Naira Miliyan 50 nan take

Atiku ya ziyarci ‘Yan gudun hijira, ya gwangwaje su da kyautar Naira Miliyan 50 nan take

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Benuwai, inda ya tuna da Bayin Allah da suke gudun hijira
  • Mai girma gwamna Samuel Ortom jihar Benuwai ya karbi bakuncin Atiku Abubakar da mutanensa
  • Ortom ya ce an dade ana jiran zuwan Atiku wanda ya ce karatun da yake yi a waje ya hana shi zuwa

Benue - Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa Atiku Abubakar ya kai ziyara zuwa jihar Benuwai, bai bar garin basai da ya yi gagarumar kyauta.

Alhaji Atiku Abubakar ya bada gudumuwar Naira miliyan 50 domin a dauki dawainiyar ‘yan gudun hijira watau IDPs da suke tarwatse a jihar Benuwai.

Mai girma gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ne ya karbi Atiku Abubakar da sauran tawagar yakin neman zabensa a garin Makurdi a ranar Lahadin nan.

Kara karanta wannan

Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata 2 daga haduwa da su a hanyar kauye

Atiku Abubakar ya bada uzurin cewa ya gagara ziyartar jihar a lokacin da suke fama da matsalar rashin tsaro ne saboda ya je kasar waje domin karo karatu.

Amma duk da haka, ‘dan siyasar ya bada kyautar Naira miliyan 50 domin a kula da wadanda suke gudun hijira domin a magance matsalolin da suke fuskanta.

A baya Gwamnan ya fadawa tsohon mataimakin shugaban kasar cewa mutanen Benuwai ba su ji dadin yadda ya yi watsi da su a lokacin da suke cikin ha’ula’i ba.

Atiku ya ziyarci ‘Yan gudun hijira, ya gwangwaje su da kyautar Naira Miliyan 50 nan take
Atiku ya ziyarci Benuwai Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

“Tun tuni ya kamata a ga zuwan ka Benuwai a matsayinka na mai sarautar ‘Zege Mule U Tiv’. Amma tun da ka zo yanzu, ya fi a ce ba a zo ba gaba daya.”
“Nan a gida ka ke, mu na murna da tarbarka. Amma bari in fada maka, mutane ba su ji dadin rashin zuwanka a lokacin da Fulani suke kashe mutane ba.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

-Samuel Ortom

Zargin da ake yi wa Fulani

Sun ta rahoto Atiku yana cewa bai yarda da yadda wasu su ke kokarin yi wa Fulani kudin-goro ba, ana neman a nuna cewa dukkaninsu mutane ne masu zubar da jini.

Waziri na Adamawa ya ce sun shawo kan ta da shi da Gwamna Ortom a kan wasu kalamai da yayi a baya.

Ortom ya ce Fulani daga waje irinsu ‘Yan Miyetti Allah Kautal Hor da Fulani Nationality Movement (FUNAM) suka addabe su, ba asalin mazaunan Benuwai ba.

Siyasar 2023

An ji cewa bisa dukkan alamu, Farfesa Yemi Osinbajo ya kauda ido daga masu zarginsa da neman cin amanar wanda ya taimaka masa a siyasa watau Bola Ahmed Tinubu.

Farfesa Yemi Osinbajo zai nemi tikitin jam'iyyar APC a zaben 2023, kuma babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya tofa albarkacinsa game da wannan nufi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel