Buhari ya yi alkawarin shiga tsakanin Hukumar EFCC da Sanatan APC da aka taso a gaba

Buhari ya yi alkawarin shiga tsakanin Hukumar EFCC da Sanatan APC da aka taso a gaba

  • Sanatan Imo ta yamma, Rochas Okorocha ya yi zama da shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa
  • Rochas Okorocha ya bukaci shugaban Najeriya Buhari ya sa baki a shari’arsa da hukumar EFCC
  • Tsohon gwamnan ya ce EFCC ta na cigaba da bincikensa duk da cewa Alkali ya taka masu burki

FCT, Abuja - Jaridar Daily Trust ta rahoto Sanata Rochas Okorocha ya na cewa ya yi alkawarin bibiyar binciken da hukumar EFCC ta ke yi masa.

Rochas Okorocha ya yi wannan bayani ne da yake zantawa da manema labarai bayan haduwarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa.

Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce hukumar EFCC na cigaba da matsa masa lamba duk da cewa kotu ta bada umarni a daina bincikensa da ake yi.

Kara karanta wannan

Zargin handamar N2.9b: Ka tsawatar wa EFCC, Okorocha ga Buhari

Sanata Okorocha yake cewa ya zauna da Mai girma shugaban kasa ne da nufin a san yadda za ayi EFCC tayi masa adalci domin an karbe masa fasfo.

A cewar ‘dan siyasar, nauyin shugaban kasa Buhari ne ya tabbatar an yi wa ‘yan kasa adalci.

Buhari da Sanata Okorocha
Rochas Okorocha tare da Shugaban kasa Hoto: NTA
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Shugaban kasa ya ce zai bibiyi lamarina zuwa gaba, musamman da ya ga hukuncin da kotu tayi. Ya ce zai bibiya ya ga asalin abin da yake faruwa.”
“Ina kuma fata zai yi hakan, na yi imanin cewa zai yi wannan.” – Rochas Okorocha.

Da aka tambaye shi a game da silar bincikensa da hukumar ta EFCC ta ke yi, ‘Dan majalisar tarayyan ya ce akwai siyasa a lamarin saboda takararsa.

Adalci na ke nema - Okorocha

“Na zo nan ne domin in nemi a yi mani adalci a matsayinsa na shugaban Najeriya. Ya kamata ya san abin da yake faruwa. Ban ce ka da a bincike ni ba.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

“Wannan ba shi ba ne abin da na ke so. Akwai hukuncin da aka yi a kasa. Ina kiran shugaban kasa wanda ya ke nada mukami a EFCC, ya ja masu kunne.”

- Rochas Okorocha.

Karin kudin makaranta

A ranar Larabar nan ne aka ji cewa shugaban majalisar tarayya, Ahmad Lawan ya yi alkawari cewa Sanatoci ba za su zura idanu a laftawa dalibai kudin karatu ba.

Sanata Ahmad Lawan ya ce a matsayinsu na Sanatoci kuma wakilan da ke wakiltar al'umma, za su sa ido domin a hana a kara kudin makarantun jami'o'in kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel