An kuma: Matashi ya rushe tarihin shekaru 60 a ABU, ya gama da abinda ba'a taba yi ba

An kuma: Matashi ya rushe tarihin shekaru 60 a ABU, ya gama da abinda ba'a taba yi ba

  • An sake samun rugujewar tarihi a Jami'ar Ahmadu Bello yayin da matashi daga sashin kimiyyar aikin gona ya gama da sakamako mai kyau
  • Mufid Suleiman ya kammala karatunsa na digirin farko a jami'ar tare da kusan cikakken makin CGPA da ya kai 4.96 a cikin tsarin makin digiri na 5.0
  • Hazikin dalibin ya shahara wajen shirya ajujuwan koyarwa da yawa ga abokan karatunsa da kannensa na karatu yayin da yake jami'ar

Wani matashi mai suna Mufid Suleiman ya kafa tarihi a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya kammala da CGPA na karshe da 4.96 a tsarin 5.0.

Abusites ya bayar da rahoton cewa sakamakon da Mufid ya samu na nufin ya ruguza wani tarihi na shekaru 60 da aka yi a cibiyar - tun lokacin da aka kafa ta a 1962.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Mufid, dalibin da ya kafa tarihi a ABU
An kuma: Matashi ya rushe tarihin ABU na shekaru 60, ya fita da sakamako mafi kyau | Hoto: abusites.com
Asali: UGC

Kafar watsa labaran da aka ambata a baya ta nuna cewa, hazikin dalibin da ya kammala karatun digirin farko a kimiyyar noma ya zarce na wani dalibi Nuhu Ibrahim da ya taba kafa irin wannan tarihi lokacin da ya samu CGPA 4.94.

Mufid yakan shirya darasi ga abokan karatunsa

Mufid wanda a 2017 ya samu karramawa daga ofishin jakadanci na kasar Sin da jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria bisa ga bajintar da ya nuna a fannin ilimi, an ce a wasu lokuta yakan shirya wa abokan karatunsa da kananan dalibai darasi lokacin da yake jami’ar.

Kuma bai tauye darasinsa ga iyaka 'yan tsangayarsu ba yakan koyar da dalibai daga wasu tsangayoyin daban-daban na jami'ar.

Legit.ng ta samu labarin cewa matashin ya samu lambar yabo ta ‘First Class Award’ daga kungiyar daliban aikin gona ta Najeriya (NASS) da ke jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 2018.

Kara karanta wannan

1st Class: Bahaushiya a jami'ar ABU ta kafa tarihin da ba a taba ba a fannin Mathematics

Bahaushiya a jami'ar ABU ta kafa tarihin da ba a taba ba a fannin Mathematics

A wani bangareb, tun lokacin da aka kafa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1962, babu wata daliba mace da ta gama digiri da 1st class a fannin lissafi. To, wannan tarihin mai shekaru 60 ya rushe da wata baiwar Allah wacce aka fi sani da Zainab Bello.

Zainab ta gama da CGPA mai ban sha'awa na 4.85, tarihin da ba a taba samu ba. An kafa Sashen Lissafi na ABU ne a shekarar 1962, a shekarar ne aka kafa jami'ar.

Fara samun nasara irin wannan ba bakon abu bane a wurin Zainab. Wani rubutu da Mohammed Ali ya yi a Facebook ya nuna cewa a dama ta kasance mai kwazo tun lokacin karatunta na nasire.

A baya kunji cewa, a ‘yan shekarun nan, mata sun dage a harkar boko kuma su na yin zarra. A wannan rahoto mun tattaro wasu daidaikun matan da suka zama zakaru.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

A jerin za a ji labarin Musa Muminah Agaka, Zainab Bello da kuma Malam Asmau Jibril.

Asali: Legit.ng

Online view pixel