Takarar 2023: Atiku, Saraki, Tambuwal sun karbi mummunan labari daga jigo a Kudu

Takarar 2023: Atiku, Saraki, Tambuwal sun karbi mummunan labari daga jigo a Kudu

  • Cif Edwin Clark, shugaban kabilar Ijaw, ya ci gaba da cewa yankin Kudu ne zai samar da shugaban kasa a 2023
  • Don haka Clark ya yi kira ga ‘yan siyasar Arewa daga jam’iyyun PDP da APC da su yi watsi da aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa
  • Dattijon ya yi wannan kira na musamman ga Gwamna Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Atiku Abubakar

Najeriya - An shawarci Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da su janye aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Shugaban kabilar Ijaw a Kudancin Najeriya, Cif Edwin Clark ne ya ba da shawarar kyauta a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 31 ga watan Janairu, jaridar Punch ta ruwaito.

Da yake caccakar ’yan siyasar Arewa da ke son tsayawa takarar shugaban kasa, dattijon ya bayyana cewa dole ne su fahimci cewa akidar shugabancin karba-karba na da matukar muhimmanci ga hadin kan kasa da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Shugaban kabilar Ijaw, Edwin Clark
Takarar 2023: Atiku, Saraki, Tambuwal sun karbi mummunan labari daga jigo a Kudu| Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Don haka, Clark ya yi kira ga Atiku, Saraki, da Tambuwal da su amince da cewa lokaci ya yi da shiyyar Kudu za ta samar da shugaban Najeriya na gaba, in ji rahoton The Cable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tunatar da ’yan Arewa cewa hatta jam’iyyar PDP da suke cikinta ta amince da tsarin karba-karba a ofisoshi daban-daban domin samun cikakken wakilci da tasiri a siyasar kasar.

Clark ya ce a cikin bayaninsa:

“Raba ofisoshin siyasa, musamman ma shugabancin kasa, shi ne maganin rugujewar Najeriya, kuma maganin zaman lafiya da hadin kan kasa.
“Abu ne sananne cewa manyan jam’iyyun kasar nan guda biyu, APC da PDP, suna bin tsarin shiyya-shiyya da karba-karba a tsakanin Arewa da Kudu.
“A 2023, kenan Arewa za ta sake yin mulki na tsawon shekaru 8. Don haka yana a hankalce da kuma daidai ne a nace cewa shugabancin kasar nan ya karkata zuwa Kudu. Bamu damu daga APC ko PDP aka samar da shugaban kasa ba tun 2015.

Kara karanta wannan

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

Wuyan Abokin takarar Atiku a zaben 2019 ya yi kauri, zai nemi Shugaban kasa a 2023

A wani labarin, idan har jam’iyyar PDP ta kai takarar shugaban kasa zuwa bangaren kudancin Najeriya a zaben 2023, tsohon gwamna Peter Obi zai nemi takara.

Peter Obi wanda ya yi takara tare da Atiku Abubakar a zaben da ya wuce, ya nuna cewa zai iya fitowa neman shugabancin Najeriya a zaben 2023 da za ayi.

Obi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a safiyar Talatar nan, 1 ga watan Fubrairu 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel