An bankado asalin dalilan da suka sa Gwamnatin Buhari ta fasa kara farashin fetur a 2022

An bankado asalin dalilan da suka sa Gwamnatin Buhari ta fasa kara farashin fetur a 2022

  • Gwamnatin tarayya ta hakura da batun janye tallafin man fetur duk da an sa hannu a dokar PIA
  • Rahotanni sun bayyana cewa dole ce ta sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki yarda da karin
  • Idan farashin fetur ya tashi, za a gamu da zanga-zangar da ya fi na #EndSARS muni a shekarar nan

Abuja - Bayanai su na zuwa a game da yadda shawarwarin tsaro suka tursasa gwamnatin Muhammadu Buhari ta lashe aman da tayi a kan tallafin fetur.

Jaridar Punch ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hakura da maganar janye tallafin man fetur bayan ya yi la’akari da wasu shawarwari da ya samu.

Bayanan da jami’an tsaro suka ba Mai girma shugaban kasa shi ne za a barke da zanga-zangan da ya fi na EndSARS kamari idan har farashin man fetur ya tashi.

Kara karanta wannan

Mukarraban Buhari su na jiran matsayarsa a kan takarar Osinbajo, Tinubu a zaben 2023

Wani jami’i da ya zanta da Punch ya ce da farko Muhammadu Buhari ya yi niyyar dabbaka sabuwar dokar IPA wanda zai jawo litar man fetur ya kara tsada.

Jami’in da bai bari a kama sunansa ba ya ce gwamnatin tarayya ta ji tsoron ‘yan adawa su yi amfani da wannan zanga-zanga, su kawowa APC matsala a 2023.

Gwamnatin Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

Rahoton da aka kai wa shugaban kasa

“’Yan sanda, DSS, NIA da ofishin NSA su kan aika rahoton tsaro ga shugaban kasa a game da abubuwa irinsu tallafin man fetur.”
“Rahoton da aka aikawa shugaban kasa ya nuna kungiyoyi su na shirin yin zanga-zangar da ya nunka na EndSARS kusan sau goma.”
“Ana hasashen litar man fetur zai tashi zuwa N350 idan farashi ya cigaba da tashi a kasuwar Duniya. Hakan zai jawo zanga-zanga.”

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

“Sun kuma jawo hankalin shugaban kasa a kan juyin-mulkin da ake ta yi a kasashen Afrika da yadda ‘yan adawa ke amfani da damar.”
“Wannan ya sa shugaban Najeriya ya dakatar da cire tallafin, ya bar wa duk gwamnatin da za ta zo wannan nauyi.” - inji majiyar.

Zanga-zangar #EndSARS

A shekarar 2020 an yi fama da zanga-zanga da bore a wasu yankunan Najeriya domin nuna rashin jin dadin yadda dakarun SARS suke cin zarafin mutanen kasar nan.

A wancan lokaci, kungiyar MURIC mai wayar da kan jama’a game da hakkokin musulmai, ta gargadi masu shiga zanga-zangar da su yi hattara da mugun nufin wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel