MURIC ta ce ya kamata a tsaida zanga-zanga tun da IGP ya ruguza SARS
- The Muslim Rights Concern, ta tsoma bakinta a game da zangar-zangar #EndSARS
- Kungiyar da aka fi sani da MURIC ta ce ya kamata masu zanga-zangar su hakura
- Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya ce ayi hattara da masu wata boyayyar manufa
MURIC ta yi magana a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020, ta na kiran a dakatar da zanga-zangar #EndSARS da ake yi a bangarorin kasar nan.
MURIC mai wayar da kan jama’a game da hakkokin musulmai, ta gargadi masu wannan zanga-zanga da cewa su yi hattara da mugun nufin wasu.
Kungiyar ta ja-kunnen wadanda ke wannan zanga-zanga da cewa su bi sannu ka da ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen cin ma manufarsu ta boye.
KU KARANTA: Hadimin Shugaban kasa ya yi martani a kan #EndSARS
Shugaban wannan kungiya na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya fitar da jawabi jiya a Legas.
Farfesa Ishaq Akintola ya yaba da kokari da jajircewar wadannan masu zanga-zanga a kan irin ta’adin da wasu jami’an ‘yan sanda su ke yi a Najeriya.
Ishaq Akintola ya fitar da jawabi, ya ce: “Mu na tir da kisan gillar da SARS su ke yi wa matasa a Najeriya, kuma mu na daukar wannan a matsayin laifi.”
Ya ce: “Masu zanga-zangar sai su koma gida yanzu, dole wadanda su ka shirya wannan zanga-zanga su yi abin da ya dace, domin babu dalilin a cigaba.”
KU KARANTA: Sojoji sun yi luguden wuta a Katsina
Farfesan ya ke cewa babu dalilin kyale wannan zanga-zangar lumuna ta #EndSARS ta rikida ta zama wata tafiya dabam da za ta iya haifar da matsala.
A karshe, MURIC ta gargadi ‘yan siyasa da bata-gari da su guji cusa son-kai a cikin harkar, sannan ya yaba da matakin da gwamnatin kasar ta yi wuf ta dauka.
A ranar Laraba kun ji cewa uwar-bari ta sa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya saduda bayan masu zanga-zanga sun ci karfinsa a cikin birnin Fatakwal.
Gwamnan ya yi yunkurin haramta zanga-zangar EndSARS a jiharsa, amma abin bai yiwu ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng