Hankali na ba kwance ya ke a kasar nan ba, Rukayya Indimi-Dantata ta koka

Hankali na ba kwance ya ke a kasar nan ba, Rukayya Indimi-Dantata ta koka

  • Diyar biloniya Mohammed Indimi kuma sirikar Dantata, Rukayya Indimi-Dantata, ta sanar da halin da ta ke ciki a kasar nan
  • A cewar mahaifiyar yara ukun, hankalin ta ba kwance ya ke ba a kasar nan kuma ta yi addu'ar Allah ya taimake mu baki daya
  • Wallafar ta ba ta rasa alaka da kisan yarinya mai shekaru 5 da malamin makaranta Abdulmalik Tanko ya yi a birnin Kano

Kano - Rukayat Indimi-Dantata, diyar fitaccen biloniyan Borno, Mohammed Indimi, ta bayyana cewa hankali ba ya kwance a kasar nan.

Mahaifiyar yara ukun wacce ta ke zama a birnin Kano, ta bayyana hakan a shafin ta na Instagram a ranar Lahadi.

Akwai yuwuwar wallafar ta yi ta ne domin martani kan sata da kisan wulakancin da aka yi wa yarinya mai shekaru biyar, Hanifa a Kano.

Hankali na ba kwance ya ke a kasar nan ba, Rukayya Indimi-Dantata ta koka
Hankali na ba kwance ya ke a kasar nan ba, Rukayya Indimi-Dantata ta koka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An sace Hanifa a watan Disamban shekarar da ta gabata, kuma malamin makarantar bokon da ta ke zuwa ne ya sace ta tare da bukatar naira miliyan shida na kudin fansa, Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai, ya fara karbar wasu kudi, yayin karbar cikon kudin fansan ne jami'an tsaro suka cafke wanda ya sace ta, a nan ne ya sanar da cewa ya kashe ta tuni.

A yayin wallafar a shafin ta na soshiyal midiya, Indimi Dantata ta wallafa, "Hankali na ba kwance ya ke a kasar nan ba. Allah ya taimake mu baki daya."

Aiki ga mai yin ka: Sanata Shekarau ya magantu kan kisan Hanifa, ya sha muhimmin alwashi

Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya sha alwashin daukar mataki da kan sa kan kisan gillar da aka yi wa Hanifa, yarinyar da aka yi garkuwa da ita kuma daga bisani aka kashe a Kano.

Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar da Hanifa ke zuwa, ya tabbatar da kashe yarinyar bayan ya yi garkuwa da ita a watan Disamba, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takardar da hadiminsa na fannin yada labarai, Sule Yau Sule ya fitar a shafin sa na Facebook, Shekarau ya jajanta wa iyayen yarinyar tare da shan alwashin sai ya bi mata khadin ta.

Shekarau ya yi fatan Allah ya bai wa iyayen Hanifa juriya da hakurin wannan rashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel