Yayin da ake kukan karancin wutar lantarki a Najeriya, an samu baraka ta kara yin kasa

Yayin da ake kukan karancin wutar lantarki a Najeriya, an samu baraka ta kara yin kasa

  • Gwamnatin Najeriya ta ce samar da wutar lantarki ya ragu zuwa megawatts 2,500 da ba a taba samu ba sakamakon ayyukan barna a bangaren
  • Hakan ya shafi manyan kamfanonin wutar lantarki a Fircados, Olorunsogo, Omotosho, Sapele Ihovbor, Geredu da Ugheli a fadin kasar
  • Najeriya ta ba da sanarwar takaita iskar gas a watan da ya gabata saboda raguwar matakan matsi da watakila suka jawo lalacewar wutar

Abuja - Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce karancin wutar lantarkin da ake fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon barna a wasu kamfanonin da ke amfani da iskar gas a fadin kasar nan.

Barna a bututun Trans-Forcados a watan Disamba ya shafi manyan tashoshin wutar lantarki da suka hada da Olorunsogo, Omotosho, Sapele, Ihovbor, Geregu da Ugheli.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige mayakan IPOB tare da tarwatsa sansaninsu a daji, sun kwato makamai

Wutar lantarki ta sake rikicewa kan bayan samun wata baraka
Yayin da ake kukan karancin wuta lantarki a Najeriya, an samu baraka ta kara yin kasa | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Barnar ta shafi bangarori da yawa

Kazalika barnar ta afkawa bututun TotalEnergies wanda ya gurgunta tashar wutar lantarkin Alaoji mai karfin megawatts 504.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa kasar ta bayar da sanarwa a watan da ya gabata cewa za ta takaita iskar gas da ke haifar da matsalar sakamakon raguwar matakan matsi da ka iya kaucewa rugujewar iskar gas.

Toshewar isassun hanyoyin wutar lantarki da rarraba wutar lantarkin ya kai akalla megawatts 2,248.50 a tsakankanin yadda ake samarwa gidaje da masana'antu.

Bangaren wutar lantarki na aiki ne da tashoshi masu amfani da iskar gas, watakila Najeriya ta damu da kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu da ya sanya wutar lantarki ya tsaya a megawatt 4,000 a ‘yan shekarun da suka gabata.

A wani bangaren, gwamnatin tarayya ta sanar da kara kudin mitar wutar lantarki masu layi daya da uku wanda zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

FG ta rantsar da kwamitin zartarwa na hukumar yaki da rashawa, EFCC

Ta sanar da hakan ne a cikin wata takarda mai kwanan wata 11 ga watan Nuwamba 2021, jaridar Punch ta rahoto.

Hukumar kula da tsarin wutar lantarki ta Najeriya ce ta fitar da sanarwar zuwa ga dukkan manyan manajoji, kamfanonin wutar lantarki da kuma dukkanin masu kula da mitoci.

Sanarwar mai lamba NERC/MAP/GEN/751/2, na dauke da taken ‘Bita kan farashin mitocin wutar lantarki karkashin tsarin kula da mita ta kasa’.

Jerin yankunan da za su fuskanci rashin wutar lantarki a Najeriya

A wani labarin, gidaje masu yawa na Najeriya ya zama dole su gyara janaretocinsu yayin da suke shirin shiga sabuwar shekara saboda yawan wutar da kasar ke samarwa ta ragu da kashi talatin.

A ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, Kamfanin samar da wutar lantarki, TCN, ya nuna cewa wutar lantarkin da kasar nan ke samarwa ta ragu zuwa 3,535.02MW, mafi karanci a cikin kwanakin nan.

Wannan al'amarin kuwa ya tada hankalin kamfanin samar wutar lantarkin na Najeriya wanda ke tura wutar ga kamfanonin rarrabe wutar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sabon nau'in cutar Shan Inna ta kama mutum 395 a jihohi 27 na Najeriya da FCT

Asali: Legit.ng

Online view pixel