Mun kashe N200m amma a banza: 'Yan Zamfara sun nemi tallafin dakile 'yan bindiga

Mun kashe N200m amma a banza: 'Yan Zamfara sun nemi tallafin dakile 'yan bindiga

  • Mazauna wani yanki a jihar Zamfara sun koka kan yadda 'yan bindiga a yankin suka addabi mazauna da hare-hare
  • Sun yi zanga-zanga a kofar gidan gwamnati, inda suka bayyana irin kokarin da suke yi amma a banza ya zuwa yanzu
  • Sun nemi gwamnati ta sa hannu wajen dakile hare-haren 'yan bindigan da kuma tura sojoji zuwa yankin

Jihar Zamfara - Mazauna yankin Nuhuche da ke jihar Zamfara sun bukaci gwamnatin jihar da ta tallafa wajen magance hare-haren da ‘yan bindiga ke ci gaba da kaiwa yankin, The Cable ta rahoto.

A ranar Lahadi ne al’ummar yankin suka gudanar da zanga-zanga zuwa gidan gwamnati domin neman gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da ya tallafa a samo mafita kan sace wasu mutane 13 da aka yi a yankin kwanan nan.

Kara karanta wannan

Zamfarawa sun yi zanga-zanga saboda tsanantar kashe-kashe a yankunan su

Taswirar jihar Zamfara: An yi zanga-zanga
Mun kashe N200m amma a banza: 'Yan Zamfara sun nemi tallafin dakile 'yan bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Musa Abdullahi, daya daga cikin al’ummar yankin, ya ce sun zo ne domin neman taimakon gwamnati domin ceto mutanen da aka sace, inda ya ce al’umar yankin sun shiga mawuyacin hali a cikin shekaru biyu da suka wuce.

A cewar Abdullahi:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun sha fama da hare-hare sama da 13, mun rasa mutane sama da 50, kuma ya zuwa yanzu, mun kashe sama da Naira miliyan 200 a cikin shekaru biyun da suka gabata a matsayin kudin fansa da kuma kirkirar kungiyoyin ‘yan banga, amma duk abin ya ci tura.
“Al’amarin ya ci gaba da kara muni, duk da kashe sama da Naira miliyan 200 wajen biyan kudin fansa da kuma kirkirar ‘yan banga.”

Sai dai, rahoton Daily Trust ya ce Abdullahi cewa yayi an kashe kusan N100m sabanin rahoton da The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka kama wani mutum da ke cin hanjin 'yan adam a Zamfara

A cewar Abdullahi, biyar daga cikin wadanda aka sace an sace su ne kwanaki 33 da suka gabata, kuma an biya kudi Naira miliyan 5 kamar yadda ‘yan bindigan suka bukata amma suka ki sakinsu inda suka sake neman babura guda biyu.

Ya kara da cewa:

"A yayin da suke kokarin biyan bukatun na babura, 'yan bindigar sun sake farmakar yankin tare da yin garkuwa da wasu mutane takwas."
"Har yanzu ba su kira ba ko bayyana wata bukata daga al'ummar yankin ba. Muna jira.”

A cewar rahoton NAN, Abdullahi ya kuma ce sama da mutane 300,000 ne suka bar Nahuche saboda hare-haren.

Ya kara da cewa:

“Mun amince da kokarin gwamnatin jiha da na tarayya wajen tunkarar kalubalen tsaro. Sai dai al’ummar Nuhuche na bukatar taimako cikin gaggawa don hana garin zama kufayi.
"Muna kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su tura sojoji yankin don taimakawa lamarin, kafin 'yan bindigar su mamaye kauyukan."

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki gari a Katsina, sun sanya harajin N10,000 kan kowa

'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa

A wani labarin, makonni biyu bayan kai farmaki ofishin wata jaridar yanar gizo da gidan talabijin, wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne a ranar Juma'a sun kai mummunan farmaki kan mai sukar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara inda suka ragargaza motarsa a Gusau.

An lakada wa Shamsu Kasida mugun duka kuma an farfasa motarsa yayin da ya tsaya a wani wurin cin abinci da ke kusa da gidan gwamnatin jihar a Gusau, Premium Times ta ruwaito.

Manajan daraktan gidan talabijin na Thunder Blowers, Anas Anka, ya zargi gwamnan jihar da daukar nauyin farmakin farko. Ya ce a tuhumi gwamnan a duk lokacin da mummunan lamari ya faru da shi ko ma'aikacinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel