Innalilahi: Yan bindiga sun halaka mutum sama da 30, sun kona kauyuka a jihar Neja

Innalilahi: Yan bindiga sun halaka mutum sama da 30, sun kona kauyuka a jihar Neja

  • Miyagun yan bindiga sun kona gidajen mutane baki ɗaya a wani mummunan hari da suka kai kauyuka biyu a jihar Neja
  • Wani da aka kashe mutum 10 daga iyalansa, ya bayyana cewa zuwa yanzun sun sake gano wasu gawarwaki na daban 20 a cikin jeji
  • Kwamishinan yan sandan jihar yace tuni hukumarsu ta ɗauki matakin tura jami'anta yankin domin saita komai

Niger - A wani hari mai kama da ɗaukar fansa, yan bindiga sun farmaki ƙauyuka biyu a jihar Neja, sun kashe mutum 37, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Makonni kalilan da suka shude, wasu Mafarauta da yan Bijilanti suka kashe dandazon yan bindiga, waɗan da ake zargin sun hana zaman lafiya a kauyukan.

Yan ta'addan sun ƙaddamar da mummunan nufin su kan kauyukan Nakuna da kuma Wurukuchi lokacin da mutanen kauyen ke gona.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun sace dagacin ƙauye, wasu ƴan ƙasar waje 2 da wasu mutane 9

Yan bindiga
Innalilahi: Yan bindiga sun halaka mutum sama da 30, sun kona kauyuka a jihar Neja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun kone baki ɗaya gidajen dake kauyen Nakuna, a kokarin su na neman yan bijilanti.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutum nawa suka mutu a harin?

Wani mazaunin kauyen, Yahya Mota, wanda ya yi rashin mutum 10 daga cikin iyalansa, yace an gano wasu gawarwaki 20 a cikin jeji bayan harin.

Mutumin yace:

"Bayan harin Nakuna, mun gano gawarwakin mutum 10 yan gida ɗaya da kuma wasu mutum 20 na daban a cikin jeji."
"Haka nan kuma a ƙauyen Wurukuchi, an kashe mutum hudu yan gida ɗaya yayin da suka je gona."

Ya ƙara da cewa bayan kashe mutane, maharan sun kone gidajen su baki ɗaya, kuma sun ƙone kayayyakin abincin su.

A cewarsa, a kokarin binciko mambobin kungiyar Bijilanti da Mafarauta. maharan sun yi awon gaba Mafarauta na musamman uku.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

Kwamishinan yan sandan jihar, Monday Kuryas, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da aka tuntube shi, yace har yanzu yan sanda ba su gano alkaluman mutanen da suka mutu yayin harin ba.

Ya ƙara da cewa tuni hukumar yan sanda ta tura jami'anta yankunan da harin ya shafa domin dawo da zaman lafiya.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya aike da tawagar wakilai Zamfara kan kashe dandazon mutane kwanan nan

Wakilan gwamnatin tarayya sun dira Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ranar Laraba, domin jajantawa gwamnatin jihar bisa harin yan bindiga na kwanan nan.

Tawagar wakilan karkashin jagorancin Ministan tsaro, Bashir Magashi, ta kunshi, ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, da kakakin Buhari , Malam Garba Shehu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel