Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100

Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100

- Masu baburan adaidaita-sahu a Kano sun fara yajin aiki saboda harajin N100 a kullum da gwamnati ta saka musu

- Yajin aikin ya jefa yan makaranta da wasu ma'aikata da dama cikin mawuyancin hali inda suka rika takawa da kafa zuwa inda za su tafi

- Masu adaidaita-sahun sun koka kan cewa wannan matakin da suka dauka ya zama dole saboda abinda suka kira kwace da ake musu da sunan haraji

Fasinjoji a birnin Kano sun shiga mawuyacin hali saboda yajin aikin da masu adaidaita-sahu suka fara a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Sun fara yajin aikin ne domin nuna rashin amincewarsu da harajin N100 a kullum da gwamnatin jihar ta kakaba musu ta hannun Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa, KAROTA, da wasu batutuwan.

DUBA WANNAN: Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa

Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100
Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Masu adaidaita-sahun sun ce wannan matakin da suka dauka ya zama dole saboda abinda suka kwatanta da kwace da sunan haraji da wasu tarar da aka karba a hannunsu.

Mafi yawancin tituna sun yi wayam duba da cewa motocin mutane masu zaman kansu, bas-bas, tasi da babura ne kawai ke yawo a titunan.

KU KARANTA: Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

Daily Trust ta ruwaito cewa mafi yawancin mutane masu matsakaicin karfi da dalibai suna takawa a kafa ne zuwa wurin aikinsu da makarantu.

Hakan ya faru ne sakamakon rashin manyan motocin haya a jihar.

Sai dai a ranar Lahadi, gwamnatin jihar ta sanar da shirinta na shigo da sabbin motocin haya 200 biranen jihar kafin karshen shekarar 2021.

Wasu matasa da ake zargin masu adaidaita-sahun ne sun yi arangama da jami'an yan sanda a Gyadi-Gyadi a court road.

Yan sandan sun harba bindiga sama domin tarwatsa matasan da ke kokarin ganin an tabbatar da yajin aikin, inda har wasu suka fasa gilasen masu adaidaita-sahun da suka fito aiki.

Matasan sun tare hanya suna kona taya amma yan sanda sun tarwatsa su.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel