Kashe-kashen jihar Zamfara ba zai tafi a banza ba, in ji APC
- Jam'iyyar APC mai mulki ta yi martani a kan kisan kiyashin da yan bindiga suka aikatawa al'umman jihar Zamfara
- APC ta sha alwashin cewa kisan ba zai tafi a banza ba ba tare da an hukunta azzaluman da suka aikata shi ba
- Ta ce ayyana yan fashin dajin da gwamnati tayi a matsayin yan ta'adda zai ba hukumomin tsaro damar yin maganinsu ba da wasa ba
Zamfara - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta bayyana cewa kashe-kashen da ake aikatawa mutane a jihar Zamfara ba zai tafi a banza ba tare da hukunci ba, jaridar The Cable ta rahoto.
Hakan martani ne ga kisan kiyashin da yan bindigar da ke tserewa harin sojoji suka yi wa mutane musamman mata da kananan yara.
Har yanzu dai akwai sarkakiya kan yawan mutanen da aka kashe a harin, yayin da gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa kimanin mutane 58 aka kashe.
Sai dai kuma mazauna yankunan da suka tsallake rijiya da baya sun ce kimanin mutane 200 ne suka mutu a harin da aka kai kananan hukumomin Bukkuyum da Anka da ke jihar.
Tasirin ayyana yan fashin a matsayin yan ta'adda
Da yake martani kan kisan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu, sakataren labaran jam'iyyar na kasa, John Akpanudoedehe, ya ce ayyana yan bindigar a matsayin yan ta'adda zai ba hukumomin tsaro damar yin maganinsu.
Ya bayyana cewa yan ta'addan na tserewa daga mafakarsu saboda ayyukan da hukumomin tsaro ke yi, rahoton Vanguard.
Akpanudoedehe ya ce:
"Shakka babu, ayyana wadannan shaidanai, miyagu kuma masu laifi a matsayin kungiyoyin yan ta'adda zai ba hukumomin tsaronmu damar yin maganinsu da kuma dakile munanan ayyukansu a kasar.
"Kwamitin riko na APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa masoyansu sannan ya mika ta'aziyya ga gwamnati da mutanen jihar Zamfara.
"Kashe-kashen jihar Zamfara da sauran wurare ba za su wuce ba tare da an hukunta su ba. Muna yabawa tare da neman goyon baya ga sojoji da sauran jami’an tsaro wadanda farmakin da suke kai wa sansanonin ‘yan ta’addan ke tabbatar da ceto ‘yan kasar da aka yi garkuwa da su tare da kawar da miyagun.
"Tuni dama, yan ta'addan sun fara tserewa yayin da ayyukan kakkaba da dakarun soji ke yi ya fara tursasa su barin maboyarsu. Muna bukatar yan Najeriya da su sanya idanu sannan su kawo rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shi ba."
Dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai, sun ceto mutane masu yawa
A gefe guda, mun ji cewa yayin da 'yan bindiga da suke kokarin tserewa daga luguden wutar sojoji suka ratsa kauyuka, jami'an tsaron sirri na sojoji sun yi ta kokarin amso wadanda aka yi garkuwa dasu daga shugabannin 'yan bindiga.
PRNigeria ta tattaro yadda 'yan bindigan da suka riga suka firgita suka kai hari a yankunan Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara, wasu shugabannin 'yan bindiga a Shinkafi da wuraren Tsafe sun turo da wakilansu ga hukumomi inda suke neman zaman lafiya tare da cigaba da sakin wadanda suka yi garkuwa da su.
'Yan bindiga a jihar Zamfara a halin yanzu suna cikin firgici, sanadiyyar luguden wutar da sojojin Najeriya suke cigaba da yi musu bayan gwamnatin tarayya ta ayyana kungiyoyin 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng