Da dumi-dumi: Buhari zai tattauna da gidajen talabijin na Channels da NTA

Da dumi-dumi: Buhari zai tattauna da gidajen talabijin na Channels da NTA

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayyana a gidan talabijin na Channels da NTA domin wata tattaunawa
  • Fadar shugaban kasa ce ta fitar da sanarwar lokacin da shugaban zai shiga tattaunawar da za a yi yau Laraba da kuma gobe Alhamis
  • Zuwa yanzu dai ba a san abubuwan da za a tattauna akai ba, saboda sanarwar fadar shugaban kasa bata ce komai ba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayyana a ranakun Laraba da Alhamis a gidan Talabijin na Najeriya NTA.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina, ya fitar ta ce za a gabatar da hirarrakin ne a gidan talabijin na Channels da karfe 7 na dare, yayin da na NTA zai kasance da karfe 8 na dare.

Kara karanta wannan

Doyin Salami: Abubuwa 12 da ya dace a sani game da masanin da zai ceto tattalin Najeriya

Shugaban kasa zai yi hira da gidan talabijin
Da dumi-dumi: Buhari zai tattauna da gidajen talabijin na Channels da NTA | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sanarwar ta Femi Adesina da Legit.ng Hausa ta samo ta ce:

"Gidan Talabijin na Channels zai watsa hirarsa ta musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 5 ga watan Junairu, 2022 da karfe 7 na yamma.
“Hakazalika, za a sake gabatar da wata tattaunawar da shugaban kasa a gidan talabijin na Najeriya (NTA) da za a yada a ranar Alhamis, 6 ga Janairu da karfe 8 na yamma.
"Don Allah a kalla."

Ba wannan ne karon farko da shugaban zai tattauna da gidajen talabijin kan batutuwan da suka shafi kasa ba, a watan Yunin 2021, shugaban ya yi makamanciyar wannan tattaunawa.

Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

A wani labarin, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ranar Talata, 4 ga watan Janairu, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai duba maslahar 'yan Najeriya miliyan 200 wajen sakin Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

Malami, yayin wata hira da yayi da manema labarai a ranar Talata, ya bayyana cewa wannan shine abin da shugaban kasa zai yi la’akari da shi kafin amincewa da bukatar shugabannin yankin kudu maso gabas na sakin Nnamdi Kanu shugaban IPOB, inji rahoton Punch.

Ya bayyana cewa dole ne shugaba Buhari ya duba yadda amincewa da bukatar zai samar wa ‘yan Najeriya sama da miliyan 200 kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel