Cin zarafi: Kafar intanet a Indiya ta tallata yin gwanjon matan muslumai a kasar

Cin zarafi: Kafar intanet a Indiya ta tallata yin gwanjon matan muslumai a kasar

  • Kasar Indiya ta ce tana kokarin gudanar da bincike kan wani shafin yanar gizo na bogi da ke tallata mata musulmi da sunan sayarwa a kasar
  • Wani dan jarida ya ce an kirkiri gidan yanar gizon ne a dandamalin GitHub mallakin Microsoft kuma yana dauke da hotuna sama da 100 na matan musulmai
  • Jam'iyyun adawa a Indiya sun bukaci jam'iyya mai mulki da ta dauki matakin gaggawa na dakile cin zarafin mata musulmi ta yanar gizo

A cewar gwamnatin Indiya, tana binciken wani shafin yanar gizo da ya yi ikirarin sayar da mata musulmi, wanda shi ne karo na biyu cikin shekara guda da za a yi gwanjon bogi irin wannan a kasar.

CNN Business ta ba da rahoton cewa, an kirkiri shafin yanar gizon akan GitHub, wani dandali na kirkira mallakin kamfanin Microsoft, wanda masu kirkirar manhajoji ke amfani da su don ginawa da girke ayyukansu.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

A rahoton AlJazeera, an ce an ga hotunan mata 'yan kasar Indiya sama da 100 wadanda aka yi gwanjonsu don sayarwa.

Shugaban kasar Indiya: Kan batun tallan mata a Intanet
Cin fuska: Wata kafar intanet a India ta sanya hotunan matan muslumai za ta sayar | Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Amfani da mummunar kalma ta batanci ga bata

An sanya wa shafin yanar gizon suna "Bulli Bai" jimlar da ta kunshi batanci karara na kalmar azzakari a kudancin Indiya tare da kalmar da ta zama ruwan dare a arewacin Indiya mai nufin kuyanga.

Mohammed Zubair, wanda ya bude shafin yanar gizon binciken gaskiya na Indiya wato Alt News ya ce shafin ya sanya hotunan mata musulmi 100 kuma ya tabbatar da sauke hotunan dukkansu kafin a goge su.

An sauke manhajar a Intanet

Tuni dai aka ruguza shafin kuma babu wata hujja da ke nuna cewa yana da wani amfani da ya wuce gwanjon bogi don tozarta mata musulmi a Indiya, a cewar wata sanarwa da hukuma ta fitar.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

GitHub ta kuma tabbatar da cewa ta cire asusun da shafukansa a kan tsarukansa.

GitHub ya ce yana da tsare-tsarensa na dogon lokaci game da bayanan da ake yadawa da ayyukan da suka hada da tozartawa, nuna wariya, da tada hankali.

Kamfanin ya ce ya dakatar da asusun shafin na yanar gizo ne biyo bayan binciken rahotanni kan wannan mummunan aiki, wanda duk ya saba wa manufofin GitHub.

Zubair ya ce shafin ya hada da hotunan ‘yar fatutukar kasar Pakistan Malala Yousafzai da fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayon Indiya Shabana Azmi.

Yawancin 'yan jarida da masu fafutukan da suka ga hotunansu a shafin sun daura hotunan tare da rubuta kalmomin, "Your Bulli Bai of the Day is."

'Yan kasa da suka fusata sun nemi a dauki mataki

Shafukan sada zumunta sun dauki dumi, musamman a Twitter, a karshen mako. Jam'iyyun adawa sun bukaci jam'iyya mai mulki ta BJP da ta gaggauta daukar mataki kan cin zarafin mata musulmi ta yanar gizo a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Shashi Tharoor, shugaban majalisa a Indiya ya fada a shafin Twitter cewa bayar da wani a matsayin kadarar sayarwa a yanar gizo laifi ne kuma ina kira ga ‘yan sanda da su dauki matakin gaggawa.

A cewarsa, wadanda ke da hannu a cikin wannan aika aika sun cancanci fuskantar hukunci.

A cewar Ismat Ara, dama an gina shafin ne da nufin wulakanta mata musulmi da cin zarafinsu.

Ta fadi hakan ne a cikin wani korafi da ta shigar ga sashen tsaron intanet na ‘yan sandan Delhi. Ara, wacce ita ma ta ga hotonta a shafin, ta wallafa kwafin korafinta a shafin Twitter.

A wani labarin, kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya (MSSN) a ranar Lahadi ta sha alwashin yaki da hana sanya hijabi a makarantu a jihohin Kudu maso Yamma, musamman a manyan makarantu.

Amir na MSSN a yankin, Qaasim Odedeji, ne ya bayyana haka a yayin taron Musulunci na IVC karo na 111 mai taken: “How could this be” a sakateriyar MSSN da ke kan titin Legas zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Ya ce wasu masu tauye hakkin addini suna jin dadin amfani da matsayinsu wajen tauye hakkin dalibai musulmi, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel