Zamfara: Sanata Marafa ya magantu kan zarginsa da ake da alaka da 'dan bindiga

Zamfara: Sanata Marafa ya magantu kan zarginsa da ake da alaka da 'dan bindiga

  • Daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan, Abdulmuminu Moossa a jihar Sokoto
  • Sanatan ya bukaci ‘yan sandan, hukumar tsaro ta fararen kaya, DSS da sauran jami’an tsaro su gabatar da wani rahoto wanda zai tabbatar da yana da alaka da Moossa
  • Sanatan ya bayyana hakan ne a wata takarda a ranar Juma’a wacce Ofishin kamfen dinsa su ka saki, inda ya ce ya kamata jami’an tsaro su fara bincike mai zurfi akan matsalar tsaron kasar nan

Zamfara - Daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan, Abdulmuminu Moossa a jihar Sokoto.

Sanatan ya bukaci ‘yan sanda, jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro da su gabatar da rahoton da zai nuna alakarsa da Moossa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2021: Manyan farmaki 5 da 'yan bindiga suka kai wa hukumomin tsaro a fadin kasar nan

Zamfara: Sanata Marafa ya magantu kan zarginsa da ake da alaka da 'dan bindiga
Zamfara: Sanata Marafa ya magantu kan zarginsa da ake da alaka da 'dan bindiga. Hoto daga thecable.ng
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ofishin kamfen din sanatan ya saki a ranar Juma’a, ya ce lokaci ya yi da ya kamata jami’an tsaro su jajirce wurin yin bincike akan matsalar tsaron kasar nan.

“A rahoton, wanda ake zargin Abdulmuminu Moossa, dan asalin jamhuriyar Chadi, an bayyana yadda jami’an tsaron Najeriya a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, ya bayyana cewa ya san Sanata Marafa tun kusan shekaru 7 da suka gabata, kuma hakan ba komai bane face karairayin da ya yi don bata sunan sanatan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Don haka muke bukatar wadanda duk wadanda cutar sharrin 2023 ta shafe su da su daina yada karairayi su kuma bar jami’an tsaro su yi ayyukansu,” kamar yadda takardar tazo.

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

Kara karanta wannan

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

A wani labari na daban, a jiya Juma'a, hafsoshin tsaro sun samu sabon umarni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa su mitsike 'yan ta'addan ISWAP, wadanda suka maye gurbin Boko Haram a ta'addancin arewa maso gabas, kafin shekarar da wa'adin mulkinsa zai cika.

The Nation ta ruwaito cewa, Buhari ya bayar da wannan umarnin a taron majalisar tsaro da suka yi a Abuja, sa'a ashirin da hudu bayan da 'yan ta'addan suka yi ruwan makamai masu linzami a filin jirgin sama na Maiduguri kafin isar shugaban kasa garin.

Mutane masu tarin yawa sun rasa rayukansu sakamakon harba makaman masu linzami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel