Abubuwan 4 da ya kamata ka sani game da sabon kocin Super Eagles, Jose Peseiro

Abubuwan 4 da ya kamata ka sani game da sabon kocin Super Eagles, Jose Peseiro

Hukumar kwallon kafa a Najeriya (NFF) da yammacin Laraba, 29 ga Disamba ta alanta nadin Jose Peseiro a matsayin sabon kocin yan kwallon Najeriya Super Eagles.

NFF ta bayyana cewa sabon kocin ba zai fara aiki kai tsaye ba, sai bayan gasar kofin nahiyar Afrika da za'ayi a sabon shekarar 2022 a kasar Kamaru.

Legit Hausa ta tattaro muku abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da sabon kocin:

1. Dan Kasar Portugal ne

José Vítor dos Santos Peseiro dan asalin kasar Portugal ne a nahiyar Turai. An haifeshi ranar 4 ga Afrilu, 1960.

2. Tsohon mataimakin Kocin kungiyar Real Madrid

A kakar kwallon 2002/2003, an nada Peseiro matsayin mataimakin Kocin Real Madris karkashin Carlos Queiroz. Shekara daya kacal yayi a Madrid kafin ya koma aikin Koci a Sporting.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles

Abubuwan 8 da ya kamata ka sani game da sabon kocin Super Eagles, Jose Peseiro
Abubuwan 8 da ya kamata ka sani game da sabon kocin Super Eagles, Jose Peseiro
Asali: UGC

3. Ya yi kocin kasar Saudiyya da kasar Venezuela

Bayan barin Sporting, Peseiro ya yi aikin maluntan kwallo a Saudiyya, Romania da Girka, kafin aka nadashi matsayin Kocin yan wasan kwallon kasar Saudiyya a 2009 kuma ya sauka a 2011.

A ranar 4 ga Febrairu, 2020, an sake nada shi matsayin Kocin kasar Venezuela.

Ya rike wannan matsayin zuwa shekarar 2011.

4. Kungiyoyin kwallon da ya jagoranta

A rayuwarsa kawo yanzu, ya jagorancin kungiyoyi kwallin irinsu UD Santarém, GUS Montemor, Clube Oriental de Lisboa, CD Nacional, Real Madrid CF (mataimaki), Sporting Clube de Portugal, Al Hilal SC, Panathinaikos FC, FC Rapid Bucureşti, Porto, Sharjah, da SC Braga

Asali: Legit.ng

Online view pixel