Manyan ayyuka 5 da wasu gwamnonin Najeriya suka aiwatar a 2021
- Yayin da saura yan kwanaki a fita daga 2021, wasu yan siyasa na bitar abunda suka yi a shekarar
- Gwamnoni a jihohi daban-daban sun jajirce don ganin sun dandanawa al’ummarsu romon damokradiyya
- Biyar daga cikinsu sun aiwatar da manyan ayyuka a jihohinsu a 2021 domin amfanin talakawansu
FCT, Abuja - Shekarar 2021 za ta kasance mai dimbin tarihi yayin da gwamnonin Najeriya da dama suka isar da romon damokradiyya ga talakawansu.
Yayin da wasu gwamnoni ke ci gaba da ayyukansu na yau da kullun a matsayin jagororin jiha, wasu sun aiwatar da manyan ayyuka domin kafa tarihi a gwamnatinsu.
Legit.ng ta jero gwamnoni 5 da suka aiwatar da irin wadannan manyan ayyuka a 2021.
1. Sir Benedict Ayade (Jihar Cross River)
A watan Satumba, gwamnan Cross River, Sir Benedict Ayade ya gina wani katafaren makarantar horar da malamai a Biase.
An kafa shi ne domin sake horar da malamai da nufin gina su a kokarin Gwamna Ayade na sauya bangaren ilimi don cusa kwarraru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ginin ya hada da dakunan karatu na zamani da kujeru, cibiyar taro mai daukar mutum 1500, dakunan gwaje-gwaje, sutudiyo, cibiyar motsa jiki da sauransu.
2. Barista Nyesom Ezenwo Wike (Jihar Rivers)
A watan Yuni, Gwamna Nyesom Wike ya gina asibiti 'Rivers State Mother and Child Hospital' wanda ministan ilimi, Dr. Osagie Emmanuel Ehanire ya kaddamar kuma ya fara aiki nan take.
Asibitin mai gadaje 132 yana da bangaren gidajen likitoci, wanda aka kawata da dakunan haihuwa 50, dakunan aiki 6, kayyakin aiki da na duba mata da sauransu.
3. Dr. Abdullahi Umar Ganduje (Jihar Kano)
A watan Yuli, Gwamna Abdullahi Ganduje ya gina katafaren gadan sama a birnin Kano wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar.
Gadan saman ya kasance gagarumin aiki a birnin mai tsohon tarihi kuma shine irinsa na farko.
An gina shi ne da nufin saukaka zirga-zirgar ababen hawa da kuma sanya jihar cikin manyan birane a duniya.
4. Babajide Sanwo-Olu (Jihar Lagas)
A watan Disamba, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da makarantar sakandare na Elemoro wanda gwamnatinsa ta gina.
An gina makarantar a karamar hukumar Ibeju Lekki da filin kwallo mai girman 50mm. An kuma gina makarantar a fili mai fadin kadada 1.54.
Baya ga dakunan karatu 18, makarantar sakandare na Elemoro yana da ajujuwa 12, dakunan girke-girke na musamman guda shida, dakin fasaha, sutudiyon zane-zane da waka.
Sai dakin gwaje-gwaje na fasaha, da dakin na’ura mai kwakwalwa. Yana kuma da ofishoshin malamai, dakin jinya, wajen cin abinci, da bandaki sama da 30.
5. Sanata Ifeanyi Arthur Okowa (Jihar Delta)
A watan Nuwamba, Sanata Ifeanyi Okowa na Delta ya gina wata sakatariyar jiha da ya dauki dukka ma’aikatun jihar da ma’aikatansu domin rage tsadar kula da gine-gine da yawa a wurare daban-daban.
An sanya wa ginin sunan Asagba na Asaba, Farfesa Chike Edozien, kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da shi.
An yi ginin ne a fili mai fadin kadada 3.88, yana da dakunan taro tara, cibiyoyin kasuwanci 5 da kuma ma’aikatu 27.
‘Yan kasuwa sun fito zanga-zanga domin hana Gwamnatin Ganduje kara shaguna a Wambai
A wani labari na daban, ‘yan kasuwan Kofar Wambai sun buge da zanga-zanga a garin Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, a dalilin shirin kafa wasu shagun.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jama’a sun tashi da safe ne kurum suka ga ana aikin gina shagunan da za a raba ta kan hanyoyin da ake wucewa.
Masu zanga-zangar sun taru a layin Sani Buhari domin nuna rashin amincewarsu. A gefe guda kuma jami’an ‘yan sanda sun yi ta kokarin su tarwatsa su.
Asali: Legit.ng