Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta
1 - tsawon mintuna
- Gagarumin kantin saide-saide da ke Kado a babban birnin tarayya na Abuja mai suna Next Cash and Carry, ya kama da wuta
- A halin yanzu, motoci uku ke farfajiyar kantin suna kokarin kashe mummunar gobarar da ba san abinda ya tada ta ba
- Har a halin yanzu, ba a san ko gobarar ta ci rai ba duk da yadda ta ke ta balbali tare da lamushe dukiyoyi
Kado, Abuja - Fitaccen katafaren kantin Next Cash and Carry da ke Kado a babban birnin tarayya na Abuja ya na ci da wuta.
Har a halin yanzu dai, ba a gano abinda ya kawo mummunan gobarar ba yayin da Daily Trust ta ziyarci wurin da lamarin ke faruwa.
A inda lamarin ke faruwa, an ga masu kashe gobara suna kokarin kashewa. A kalla motoci uku na kashe wuta aka gani a farfajiyar kantin.
Ba a tabbatar ko gobarar ta ci rai ba har yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Karin bayani na nan tafe...
y
Asali: Legit.ng