Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

  • Hukumar kula da sufurin jiragen sama na farar hula, NCAA, ta kulle babban ofishin gagarumin kamfanin sadarwan nan mai suna Glo
  • Kamar yadda NCAA ta tabbatar, suna bin kamfanin sadarwan zunzurutun bashin kudi wanda ya kai N4.5 biliyan kuma sun ki biya
  • Darakta janar na hukumar, Kyaftin Musa Nuhu ne ya jagoranci rufe ofishin da ke Wuse 2 a birnin babban tarayya da ke Abuja

FCT, Abuja - Hukumar kula da sufurin jiragen sama na farar hula, NCAA, ta garkame babban ofishin kamfanin sadarwa na Glo da ke Wuse 2 a Abuja kan bashin N4.5 biliyan.

Darakta janar na hukumar NCAA, Kyaftin Musa Nuhu ne ya jagoranci garkame ofishin kuma ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ne ya duba yadda lamarin ya kasance, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn
Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn
Asali: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa, darakta janar na hukumar ya ce za su cigaba da wannan rufe-rufen inda zai ratsa zuwa manyan ofisoshin kamfanin sadarwan da ke kasar nan har sai kamfanin sadarwan ya biya su hakkinsu.

Karin bayani ya na nan tafe...

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel