Sarauniyar Kyau, Shatu Garko, ta mayar da martani kan masu zaginta

Sarauniyar Kyau, Shatu Garko, ta mayar da martani kan masu zaginta

  • Sarauniyar Kyau a Najeriya, Shatu Garko, ta caccaki masu sukarta kan takarar da tayi a gasar na bana
  • Shatu, a ranar 17 ga Disamba, ta zamto mace ta farko mai sanye da Hijabi da ta samu nasarar lashe wannan gasa a Najeriya
  • Hukumar Hisbah, Kungiyar MURIC da Malaman addini a fadin tarayya sun yi Alla-wadai da wannan abu

Kano - Yan kwanaki bayan rahotannin cewa hukumar Hisbah na shirin aika sammaci ga iyayen Sarauniyar Kyan Najeriya, Shatu Garko, budurwar ta yi martani mai zafi.

Punch ta ruwaito cewa a ranar Juma'a, 24 ga Disamba ta caccaki masu sukanta kan takarar da tayi a gasar a matsayinta na Musulma.

A cewarta, masu magana su cigaba da babatunsu amma fa kambin sarauniyar kyau na kanta kuma babu yadda aka iya.

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Tace:

"Babu wanda ya kirani amma an turo min sakonni da yawa inda wasu ke cewa abinda nayi bai dace ba, tsirara nake."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yan Najeriya sun fiya shisshigi da katsalandan da yiwa mutum hukunci. Wasu cewa sukayi Shugaban kasa ya biya kudi a bani kyautar; wasu suka ce Gwamnan jihata. Wasu sun ce iyaye na ne, amma duk karya ne."
"Wasu da ba Musulmi ba sun ce na batawa gasar Sarauniyar Kyau suna. Ko amsa ban basu, kawai harkar gabana nike yi. Kambun na kai na kuma babu yadda na iya."

Sarauniyar Kyau, Shatu Garko, ya mayar da martani kan masu zaginta
Sarauniyar Kyau, Shatu Garko, ya mayar da martani kan masu zaginta
Asali: UGC

Gasar Sarauniyar Kyau Tamkar Shirin BBNaija Ne, MURIC Ta Goyi Bayan Hisbah

Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC, ta goyi bayan hukumar Hisbah akan gayyatar iyayen Shatu Garko, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya a shekarar 2021, akan shigarta gasar.

Kara karanta wannan

Shatu Garko: Gasar Sarauniyar Kyau Tamkar Shirin BBNaija Ne, MURIC Ta Goyi Bayan Hisbah

Garko, wacce ‘yar asalin jihar Kano ce ta zama mace ta farko mai hijabin da ta lashe gasar tun bayan farawa a shekarar 1957.

Sai dai Haruna Ibn-Sina, kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, ya yi alawadai akan shigar Garko gasar inda ya ce hakan ya saba wa koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel