Yanzu-Yanzu: Yan Majalisa sun yi amai sun lashe kan tabbatar da kundin gyaran zabe 2021

Yanzu-Yanzu: Yan Majalisa sun yi amai sun lashe kan tabbatar da kundin gyaran zabe 2021

  • Majalisar dattawa ta fasa tsallake matakin Buhari na kin amincewa da sabon kundin zabe da suka wa garambawul 2021
  • Maimakon haka majalisar da yanke shawarar tuntubar takwararta majalisar dokoki da kuma yan Najeriya kan lamarin
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaba Buhari ya aike wa majlisun biyu wasikar dalilin ƙin rattaba hannu kan kudirin

Abuja - A ranar Laraba, yan majalisar dattawa sun canza matakin da suka fara yunkurin ɗauka na tabbatar da kundin gyaran zaɓe 2021 bayan shugaba Buhari ya ƙi amincewa.

Dailytrust ta rahoto cewa a ranar Talata, yan majalisan sun fara tattara sa hannun su kuma suka sha alwashin tsallake matakin shugaba Buhari kan kundin.

Haka nan kuma yan majalisan sun ɗage amince wa da kasafin kudin 2022, wanda suka tsara zasu yi ranar Talata 22 ga watan Disamba, domin maida hankali kan lamarin.

Kara karanta wannan

Buhari: Sanatoci na kokarin hada-kai domin gyara dokar zabe da karfi da yaji ta Majalisa

Majalisa
Yanzu-Yanzu: Yan Majalisa sun yi amai sun lashe kan tabbatar da kundin gyaran zabe 2021 Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Wane mataki za su ɗauka yanzu?

Bayan fitowa daga wani zama da suka yi na tsawon minti 40, Sanatocin sun yanke hukuncin za su tuntubi takwarorinsu na majalisar dokoki da kuma yan Najeriya kan yadda ya kamata su ɗauka.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, bayan fitowa daga ganawarsu ta sirri, ya sanar da cewa:

"Majalisa ta tattauna kan hanyoyin da ya kamata su bi na martani kan wasikar da shugaba Buhari ya aiko mata game da sabon kundin zabe da aka yi wa garambawul 2021."
"Yan majalisan sun cimma matsaya cewa su fara tuntubar majalisar dokokin tarayya a watan Janairu, lokacin da majalisun biyu za su haɗu wuri ɗaya."

A cewar Sanata Lawan, sanatoci sun cimma matsayar su nemi shawara daga mutanen mazaɓar su domin suna da rawar da za su iya taka wa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan Majalisar Wakilai sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn

Tun a jiya ne, majalisar dokokin tarayya ta tafi hutu bayan amincewa da kasafin kudin shekarar 2022, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma An maka tsohon gwamna gaban kotu kan ya ƙi neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Wasu mutum biyu a jihar Bauchi sun gurfanar da tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu a gaban kotu kan ya ki fara shirin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Masu shigar da karan sun bukaci babbar kotun Bauchi ta tilasta wa sanatan ya nemi tikitin takara karkashin kowace jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel