Da Duminsa: Mafarauta sun kame 'yan bindiga 3 bayan doguwar musayar wuta

Da Duminsa: Mafarauta sun kame 'yan bindiga 3 bayan doguwar musayar wuta

  • Wasu masu garkuwa da mutane sun shiga hannun mafarauta yayin da aka fatattakesu a maboyarsu a Kogi
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an kame masu garkuwa da mutane har uku, yayin da wasu suka tsere
  • An kuma ruwaito cewa, a halin yanzu an mika su ga jami'an tsaro, kuma sun tona asirin wasu mambobinsu

Kogi - An kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a maboyar su da ke kusa da unguwar Ossra-Irekpeni da ke kan titin Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja.

Daya daga cikin mafarautan yankin da suka kai harin ya shaida wa Daily Trust cewa an yi musayar wuta dasu.

Ya ce mafarautan tare da shugaban karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi, Joseph Samuel Omuya, sun kai farmaki dajin ne bisa samun rahoton kasancewar 'yan ta'addan a yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano

'Yan bindiga da masu sace mutane
Da Duminsa:Mafarauta sun kame 'yan bindiga 3 bayan doguwar musayar wuta | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce a lokacin da suke kutsawa dajin, masu garkuwar sun bude wuta inda mafarautan suka mayar musu da wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar majiyar:

“Nan da nan muka yi ta harbe-harbe kuma an kama uku daga cikin masu garkuwa da mutanen."

A cewarsa, wasu ‘yan tawagar ta'addan sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da wadanda aka kama aka mika su ga jami’an tsaro a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Shugaban karamar hukumar Adavi ya tabbatar da kama wasu masu garkuwa da mutanen uku, yana mai cewa shi ne ya jagoranci aikin.

Ya ce masu garkuwa da mutanen na daga cikin ’yan tawagar da ke addabar mazauna yankin da matafiya a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja.

A kalamansa:

“Daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya bayyana yadda suke gudanar da ayyukansu, da irin nagartattun makaman da suke amfani da su, ya kuma lissafa sunayen wasu ‘yan tawagar."

Kara karanta wannan

Matafiya da dama sun makale a yayin da ‘yan bindiga suka tare hanya a Neja

Shugaban, yayin da yake yaba wa mafarautan yankin bisa kokarinsu da jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu, ya bukaci mazauna kauyuka da su kasance masu kula da harkokin tsaro tare da bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro da suka dace.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran waya ko amsa sakon da aka aike masa don jin ta bakinsa.

A makon da ya gabata ma an samu nasarar kame wasu masu garkuwa da mutane har shida a wani yankin jihar ta Kogi, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Hare-hare sun yawaita a Zamfara, tawaga ta tafi ganawa da kasurgumin dan bindiga

A wani labarin, sakamakon hare-haren wuce gona da iri a yankin Shinkafi a jihar Zamfara, musamman kan matafiya dake kan hanyar da ta hada Gusau zuwa Sabon Birni, a jihar Sokoto, an aika da sabon jakada domin ganawa da kasurgumin dan bindiga, Turji.

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

A farkon watan Nuwamba, Turji ya yi watsi da tawagar Shinkafi ta neman tattaunawa, wadanda rahotanni suka ce sun je wurinsa domin neman zaman lafiya, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Alhaji Ali Mamman, ya ce an sha kai hare-hare a babbar hanyar tun bayan harin da sojoji suka kai ta sama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar iyaye da sauran ‘yan uwa na aminin Turji, Dan Bokkolo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel