Rundunar soji na bukatar sake dabarun yaki don yin nasara a kan yaki da ta’addanci - Dan majalisa

Rundunar soji na bukatar sake dabarun yaki don yin nasara a kan yaki da ta’addanci - Dan majalisa

  • Ahmadu Jaha, dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Damboa/Gwoza/Chibok na jihar Borno ya bukaci rundunar soji da ta sauya dabarun yaki da ta'addanci
  • Jaha ya kalubalanci rundunar da ta dunga kai yaki har kofar yan ta'addan maimakon jira su kawo hari kafin su dakile shi
  • Ya yi martanin ne bayan harin da ISWAP ta kai garin Askira, a karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno wanda yayi sanadiyar rasa Sojoji

Wani dan majalisar wakilai, Ahmadu Jaha, ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya na bukatar kai mummunan farmaki domin samun nasara a yakin da take yi da ta'addanci.

Jaha, dan majalisa mai wakiltan mazabar Damboa/Gwoza/Chibok na jihar Borno, ya yi magana ne a zauren majalisar wakilan a ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba.

Rundunar soji na bukatar dabarun yaki don yin nasara a kan yaki da ta’addanci - Dan majalisa
Rundunar soji na bukatar dabarun yaki don yin nasara a kan yaki da ta’addanci - Dan majalisa Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Dan majalisar na bayar da gudunmawa ne ga wani kudiri da Haruna Mshelia ya dauki nauyinsa, inda ya yi kira ga inganta yanayin tsaro a garuruwan Mandiragrau, Askira da Garkida na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Abu daya ya rage mu kawo karshen yan ta'adda da yan bindiga a Najeriya, Hafsan Soji

An tattaro cewa garuruwan na a kan iyakar Sambisa.

Legit Hausa ta rahoto yadda mayakan ISWAP suka kai farmaki garin Askira, a karamar hukumar Askira Uba ta Borno inda suka halaka wani Birgediya Janar da jami'an sojoji.

Da yake magana a ranar Talata, Jaha ya ce ya zama dole sojoji su bar wajensu sannan su kai yaki har zuwa kofofin yan ta'addan, rahoton The Cable.

Jaha ya c e:

"Ina so in jaddada bukatar canja dabaru. Ko mun so ko mun ki, ba za ku iya zama a wajenku ba kuna jiran 'yan ta'adda su kawo hari kafin ku dakile su.
"Ya kamata mu fada ma junanmu gaskiya. Idan har rundunar sojin Najeriya ta gaza samar da dabarun yaki masu zafi, wannan yakin ba zai zo karshe ba. Ya zama dole mu zafafa manufa ta hanyar kai yaki zuwa kofofinsu domin mu daidaita su. Ba za su samu kwanciyar hankali da lokacin zuwa da kai farmaki garuruwa ba.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka

"Hatta ga nasarorin da rundunar soji ta samu sakamakon mika wuya da wasu yan Boko Haram ke yi, muna sane cewa ba sakamakon ayyuka ko karfin wuta bane, ya kasance sakamakon adawa tsakanin mambobin Boko Haram masu biyayya ga Shekau da kuma masu biyayya ga dayan bangaren ne.
"Sakamakon mutuwar Shekau, wasu yan ta'adda sun yanke shawarar barin ta'addanci, wanda hakan ne ya sanya su mika wuya.
"Don haka, idan za mu yi nasara a yakin, ya zama dole rundunar sojin Najeriya ta sauya dabaru - barin waje daya don far masu."

Jaha ya ce an kashe Janar din sojan ne a tazarar kilomita 4 daga hedikwatar birgediya, inda ya kara da cewa "yan ta'addan ne suka kai harin ga sojojin".

ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce

A wani labarin, mun jin cewa jama'a masu zama wasu daga cikin kauyukan Borno sun koka da halin da suka samu kansu na tilascin biyan haraji da 'yan ta'adda suka saka musu a cikin zakkar amfanin gona.

Kara karanta wannan

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

Kamar yadda BBC ta wallafa, jama'a mazauna garin Damboa sun sanar da yadda 'yan ta'addan ke amfani da karfi wurin kwace amfanin gona da dabbobi, kuma biyayya a gare su ta zama dole domin tsira.

Wannan al'amarin ya kara fitowa ne a lokacin da ake cigaba da rade-radin cewa 'yan ta'addan ISWAP na amshe haraji daga wurin makiyaya da manoman jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel