Kano: Gwamnati za ta saya wa Sheikh Abduljabbar littafan Sahihul Bukhari da Muslim

Kano: Gwamnati za ta saya wa Sheikh Abduljabbar littafan Sahihul Bukhari da Muslim

  • Yayin zaman shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnatin jihar Kano da aka yi a babbar kotun musulunci da ke kofar Kudu, wani lamari ya auku
  • Bayan kotu ta amince malamin ya yiwa shaidu tambayoyi sai ya bude wasu littafai da ba a san su ba, hakan ya sa lauyan masu kara ya nuna rashin amincewarsa
  • Kotu ta gabatar da littafan Sahihul Muslim da Bukhari inda ta bukaci Sheikh Kabara ya siya ya ce bashi da kudi, hakan ya sa gwamnatin Kano ta amince da siya masa kafin wata ranar shari’ar

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yanke shawarar siya wa Sheikh Abduljabbar Kabara littafan Sahihul Bukhari da Muslim, Freedom Radio ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda zaman kotun musuluncin da ke zama a Kofar Kudu ya kaya bayan lauyan masu kara, Mamman Lawal Yusufari SAN ya gabatar da bukatarsa.

Kara karanta wannan

El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter

Kano: Gwamnati za ta saya wa Sheikh Abduljabbar littafan Sahihul Bukhari da Muslim
Gwamnatin Kano za ta saya wa Sheikh Abduljabbar littafan Sahihul Bukhari da Muslim. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yusufari ya nemi kotu ta amince kuma ta ba malamin damar yi wa shaidu tambayoyi.

Nan take kotun ta amince da bukatarsa. Ana tsaka da hakan ne ya dauko wani littafi don ci gaba da tambayoyin, sai lauyan masu kara ya nuna rashin amincewarsa.

Lauyan ya bukaci a san littafin da malamin ya ke amfani da shi

A cewar lauyan, ya kamata a san wanne littafi ne malamin yake kawo bayanansa. Malamin ya ce littafai 2 ne duk hade da matani da sharhi.

Mai gabatar da kara ya roki kotu da ta bayar da damar kawo littafan Bukhari da Muslim amma matani ba sharhi ba.

Bayan hakan ne malamin ya ce ya na bukatar a bashi littafan don ya duba su kafin a sake wani zaman kotun.

Mai shari’a ya ki amincewa da wannan bukatar ta shehin malamin sannan ya ce ya siya nasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa ɗan Boko Haram hukuncin kisa ta hanyar rataya

Sheikh Abduljabbar ya yi gaggawar bayyana cewa ba shi da kudi sakamakon yadda ba ya sayar da komai tun bayan tsare shi da aka yi.

Bayan jin wannan ne lauyoyin gwamnati suka ce gwamnatin jihar za ta siya wa malamin littafan sannan Malamin ya yi godiya.

Alkalin kotun ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamban 2021.

Zargin batanci: Rikici ya barke tsakanin Sheikh AbdulJabbar Kabara da Lauyoyinsa a Zaman Kotu

A baya, kun ji cewa rikici ya barke a kotun shari'ar musulunci ta jihar Kano yayin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lauyoyinsa basu kare shi a gaban kotu.

A karo na biyu shehin malamin ya zargi lauyoyinsa da rashin kareshi idan ana kawo shaida kuma basu ba shi dama ya kare kanshi.

Rahoton Dailytrust ya nuna cewa Malam Abduljabbar ya roki kotu ta bashi dama ya kare kansa tunda lauyoyinsa basu iyawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel