Kwana guda bayan harin da aka kai wa mahaifinta, 'Yar Goje ta ajiye aikin Kwamishina a Jihar Gombe

Kwana guda bayan harin da aka kai wa mahaifinta, 'Yar Goje ta ajiye aikin Kwamishina a Jihar Gombe

  • Dr Hussaina Danjuma Goje, 'Yar Sanata Goje ta ajiye aiki a matsayin Kwamishinan Muhalli da Albartakun Daji na Jihar Gombe
  • Hakan na zuwa kimanin awanni 24 bayan wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai wa tawagar mahaifinta hari a hanyarsu na zuwa Gombe daurin aure
  • Dr Hussaina ta mika godiyarta ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya bisa damar da ya bata na yin aiki a gwamnatinsa tare da cewa ta ajiye aikin dan kashin kanta ne

Gombe - Kimanin awa 24 bayan an kai wa mahaifinta hari, Dr Hussaina Danjuma Goje ta ajiye aikinta a matsayin kwamishinan muhalli da albarkatun daji na jihar Gombe.

A cikin wani gajeren sakon bidiyo da ta fitar a ranar Asabar, Hussaina ta ce ta ajiye aikin ne kan wasu dalilai na kashin kanta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

Kwana guda bayan harin da aka kai wa mahaifinta, 'Yar Goje ta ajiye aikin Kwamishina a Jihar Gombe
'Yar Sanata Goje ta ajiye aikin Kwamishina a Jihar Gombe. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Ta yi wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya godiya bisa damar da ya bata na yi wa jiharta aiki.

Ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yau Asabar 6 ga watan Nuwamban 2021, ina son sanar da al'umma da kafafen watsa labarai cewa ni, Dr Hussaina Goje na mika takardar murabus di na a matsayin Kwamishinan Muhalli da Albarkatun ga Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, na ajiye aiki daga yau."
"Ina son sanar da cewa na ajiye aikin ne kan dalilai na kashin kai na. Da haka, ina mika godiya ta ga Gwamna Yahaya da ya bani damar yin aiki a gwamnatinsa."

A dai ranar Juma'a ne wasu da ake zargin yan daba ne suka kai wa mahaifinta, Sanata Muhamamd Goje hari bayan tare tawagarsa a hanyarsu na zuwa Gombe.

Amma rahotanni sun ce babu abin da ya same shi.

Read also

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Rahotanni baya-bayan nan suna nuni da cewa, dangantakar da ke tsakanin Sanata Goje da gwamna Yahaya ta yi tsami a ‘yan kwankin nan.

'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

Tunda farko, kun ji cewa wasu da ake zargin yan daba ne, a ranar Juma'a, sun hana Sanata Muhammad Goje shiga garin Gombe.

Goje, wanda ya tafi Gombe domin halartar daurin aure, ya dira a filin saukan jirage na Gombe a Lawanti misalin ƙarfe 10.40 na safe.

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda ake zargi yan daban ne sun tare babban titin Gombe-Bauchi kusa da International Conference Centre, sun cinna wuta a titi sun hana shiga ko fita daga Gombe.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel