Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta damke Obi Cubana a ofishinta dake birnin tarayya Abuja

Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta damke Obi Cubana a ofishinta dake birnin tarayya Abuja

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta damke shahrarren dan kasuwa, Obinna Iyiegbu, wanda akafi sani da Obi Cubana.

TVCNews ta ruwaito cewa dan kasuwan ya dira hedkwatan hukumar dake unguwar Jabi misalin karfe 12 na rana har yanzu ana masa tambayoyi.

Obi Cubana ya shahara da facaka da kudi wurin bukukuwa.

Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta damke Obi Cubana a ofishinta dake birnin tarayya Abuja
Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta damke Obi Cubana a ofishinta dake birnin tarayya Abuja
Source: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karin bayani na nan tafe

Source: Legit.ng

Online view pixel