Kotu ta rufe asusun bankin wata jihar Arewa saboda taurin biyan bashin da ta ci 2008

Kotu ta rufe asusun bankin wata jihar Arewa saboda taurin biyan bashin da ta ci 2008

  • Babban kotun tarayya tace a rufe duka asusun Gwamnatin Benuwai da ke banki saboda gaza biyan wani tsohon bashi
  • Wannan hukunci da Alkali ya zartar bayan AMCON Ta shigar da kara ya shafi kamfanin HPPS Multilink Services Ltd.

FCT, Abuja - Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bada umarnin a soma rufe duk wasu asusun da gwamnatin jihar Benuwai ta ke da su a banki.

Vanguard tace Alkalin kotun tarayyar, mai shari’a Inyang Ekwo ya dauki wannan mataki ne saboda jihar ta ki biyan wasu bashi da ta karba tun 2008.

Hukumar Asset Management Corporation of Nigeria (AMCON) mai kula da kadarori da dukiyoyin gwamnati ta shigar da kara gaban Alkali Inyang Ekwo.

An hada da HPPS Multilink Services Ltd

Haka zalika, kotu tace a rufe asusun da kamfanin HPPS Multilink Services Ltd ke da shi a banki. Za a garkame akawun din kamfanin har sai an gama shari’a.

Kara karanta wannan

Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana a kotu kan zargin damfarar yanar gizo

Leadership tace hukumar AMCON ce ta shigar da kara, wadanda ake tuhuma sune gwamnatin jihar Benuwai da kamfanin HPPS Multilink Services Ltd.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Samuel Ortom
Gwamnan Benuwai mai-ci, Ortom Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Wannan mataki da Alkali ya dauka ya shafi bankuna kusan 20 na kamfanin da gwamnatin Benuwai.

Hukumar AMCON ta shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/AMC/74/2021 a ranar 30 ga watan Satumba, 2021, ta hannun lauyanta, Darlington Ozurumba.

Darlington Ozurumba ya gabatar da bukatu biyar a kotun na Abuja. Na farko a rufe asusun JAAC na hadaka da gwamnatin jihar Benuwai ta bude a bankuna.

Sannan lauyan yana so a garkame duk wasu asusu da jihar Benuwai take da shi har sai an kare shari’a.

A karshe, Inyang Ekwo ya karbi rokon Ozurumba, ya haramta ayi duk wata mu’amala da gwamnatin jihar Benuwai ta asusun da ta mallaka a bankuna.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sa gidaje, rigunan mama da gwala-gwalan Diezani Alison-Madueke a kasuwa

Alkalin ya ba bankunan kwanaki bakwai su rufe asusun da gwamnatin Benuwai ta bude. An yi alkawari za a biya bashin a shekaru biyu da kudin ruwan 19%.

Archbishop John Osa-Oni ya soki Ahmad Gumi

A jiya ne kungiyar PFN ta reshen kudu maso yammacin Najeriya ta fito tace Sheikh Ahmad Gumi ya kamata a fara zargi da laifin alaka da ‘Yan bindiga a Arewa.

Shugaban kungiyar kiristocin, Archbishop John Osa-Oni yace da a ce Sheikh Gumi kirista ne, da tuni an yi ram da shi don haka ya yi kira a dauki mataki a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel