Gwamnati ta sa gidaje, rigunan mama da gwala-gwalan Diezani Alison-Madueke a kasuwa

Gwamnati ta sa gidaje, rigunan mama da gwala-gwalan Diezani Alison-Madueke a kasuwa

  • Gwamnatin tarayya za ta yi gwanjo da kayan wasu gawurattun tsofaffin ‘yan siyasa
  • Kwamiti ya sa dukiyoyi, gwala-gwalai da gidajen Diezani Alison-Madueke a kasuwa
  • Akwai gidaje 4 na Marigayi Air Chief Marshal Alex Badeh da za a saida a garin Abuja

Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen sa kadarori da dukiyoyin wasu ‘yan siyasa, daga ciki har da tsohuwar Minista, Diezani Alison-Madueke.

Jaridar Punch ta ce daga cikin kadarorin tsohuwar Ministar man fetur din da za ayi gwanjonsu har da wasu manyan gidajenta da ke Banana Island a Legas.

Akwai kuma wani katafaren gini mai dauke da gidaje sama da 20 a unguwar Federal Government Layout.

Kayan Diezani Alison-Madueke da za a sa kasuwa

Kara karanta wannan

Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya

Rahoton yace an hada da dogayen rigunan barci 125, kananan jallabiyoyi 13, takalman fita atisaye 41, fulawa 77, rigunan kwat 11 da kuma rigunan mama 11.

Har ila yau a cikin kayan Alison-Madueke da za a yi gwanjonsu akwai gyalen lullubi sama da 73 da wasu samfurin rigunan mama har 30 da fankoki akalla biyu.

Sauran kayan na ta da za a sa a kasuwa sun hada da barguna, teburori da takalma fiye da 60. Jaridar nan ta The Cable ta tabbatar da wannan labarin a yau.

Diezani Alison-Madueke
Diezani Alison-Madueke Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gidajen Air Chief Marshal Alex Badeh

Akwai wasu gidajen tsohon hafsun tsaro na kasa, Marigayi Air Chief Marshal Alex Badeh da ke unguwannin Wuse 2 da Maitama a Abuja, da za a saida.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Kadarorin sun hada da wasu gidaje hudu da ke kan titin Adzope Crescent, Kumasi Crescent da Umme Street a unguwar Wuse a babban birnin tarayyan.

Shugaban kwamitin gwanjo da kadarorin sata na gwamnatin tarayya, Mohammed Etsu, ya fadawa ‘yan jarida mutane sun nuna sha’awar sayen kayan.

Etsu yace za ayi gaskiya wajen yin gwanjon wadannan kaya masu tsada, ya kuma ce ba a hada da gwala-gwalai ba saboda sai an gama yi masu farashi.

Muhammadu Sanusi II ya soki tallafin fetur

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya fito yace gwamnatin tarayya tana saba doka da ta ke biyan tallafin man fetur daga asusun hadaka na kasa.

Mai martaba ya zargi gwamnatin tarayya da batar da kudin Jihohi da kananan hukumomi. Sanusi II yace akwai badakala a cikin tsarin da aka kawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel