Manhajar e-Naira ta dawo kan ma'ajiyar manhajoji ta Play Store, tuni an fara sauketa

Manhajar e-Naira ta dawo kan ma'ajiyar manhajoji ta Play Store, tuni an fara sauketa

  • Bincike ya nuna cewa, manhajar eNaira ta dawo aiki tun bayan da ta bace a kan ma'ajiyar manhajojin wayoyin android ta Play Store
  • A halin da ake ciki, wasu mutane sun bayyana yadda suka ji da dawowar manhajar, inda suka bayyana sauyin da suka gani
  • Legit.ng ta yi duba ga manhajar, inda ta shaida dawowar manhajar tare da ganin martanin da mutane ke yi a kanta

Manhajar ​​e-Naira ta dawo kan Play Store na kamfanin Google awanni 24 bayan bacewarta.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa manhajar e-Naira Speed Wallet ta bace daga Play Store ranar Laraba, sa’o’i 48 bayan kaddamar da ita.

Daraktan Sadarwa na na CBN, Osita Nwanisobi, a Abakaliki, a ranar Alhamis, ya ce bacewar manhajar na wucin gadi ne kawai saboda ana ci gaba da inganta ta da nufin magance matsalolin da aka samu tun lokacin kaddamar da ita.

Kara karanta wannan

CBN ta magantu kan dalilin bacewar manhajar e-Naira a intanet, yaushe kuma za ta dawo

Yanzu-Yanzu: Manhajar e-Naira ta dawo kan ma'ajiyar Play Store
Yanzu-Yanzu: Manhajar e-Naira ta dawo kan ma'ajiyar Play Store
Asali: Facebook

'Yan Najeriya sun soki manhajar kan gazawa wajen hada sakonnin imel da BVN cikin sauki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin ya tafi na wucin gadi, sama da mutane 100,000 ne suka sauke manhajar a wayoyinsu.

Manhajar wacce ta bace a ranar Laraba da yamma, ta dawo kai tsaye da misalin karfe 1:00 na ranar Alhamis.

Binciken da aka yi ya nuna cewa har yanzu wasu 'yan Najeriya na ci gaba da yin watsi da bayanan da ba su ji dadi ba a kan manhajar saboda gazawarta wajen aikata abin da suke so.

Yayin da Legit.ng Hausa ta yi duba ga martanin mutane game da manhajar a ma'ajiyar manhajoji ta Play Store, an ga sabbin maganganu da mutane suke a kanta.

Wasu sun bayyana jin dadinsu bisa dawowar manhajar inda suka bayyana abubuwan da asuka shaida bisa dawowarta.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara zata raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP ranar Juma'a

CBN ta magantu kan dalilin bacewar manhajar e-Naira a intanet, yaushe kuma za ta dawo

The Nation ta ruwaito cewa, Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dalilin bacewar sabuwar jakar kudin intanet mallakar Najeriya wato e-Naira da aka kaddamar ba shiri daga kafar Play store na kamfanin Google.

Bankin ya bayyana cewa bacewar manhajar na wucin gadi ne kawai saboda yana fuskantar wani muhimmin ingantayya da nufin magance matsalolin da aka samu tun lokacin kaddamar da shi.

Daraktan Sadarwa na Bankin, Osita Nwanisobi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel