Tubabbun tsageru da masu tada kayar baya sun toshe hanyar shiga ofishin gwamna

Tubabbun tsageru da masu tada kayar baya sun toshe hanyar shiga ofishin gwamna

  • Tubabban tsagerun Neja Delta sun mamaye tare da toshe hanyar shiga ofishin gwamnan Cross River, Ben Ayade
  • Sun hana jami'an gwamnati, masu mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnati shiga ofisoshinsu domin nuna fushinsu
  • A cewarsu, sun yada makamai tun shekaru 3 da suka gabata amma har yanzu babu abinda suka samu daga gwamnati na tallafi

Cross River - Tubabbun tsageru masu tarin yawa daga sassa daban-daban na jihar Cross River a jiya sun toshe tare da mamaye ofishin Gwamna Ben Ayade.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, sun haramta wa jami'an gwamnati, masu mukaman siyasa da kuma manyan ma'aikatan gwamnatin da ba su shiga yajin aikin kungiyar kwadago ba shiga ofisoshinsu.

An kuma: Tsageru kuma masu tada kayar baya sun toshe hanyar shiga ofishin gwamna
An kuma: Tsageru kuma masu tada kayar baya sun toshe hanyar shiga ofishin gwamna. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC
Daya daga cikin masu magana da yawun tubabbun tsagerun ya ce: "Tun da suka roke mu kuma muka amince, mun tuba tare da mika makamanmu a shekarar 2018 bayan gwamnatin jihar ta yi mana alkawarin rangwame tare da tallafi, babu abinda muka samu.

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

"Mun halarci wasu horarwa kuma har yanzu babu jarin da ya iso mana. Gwamnatin jihar ba ta yi wani aiki ba, ba mu cikin farin ciki. Kada su dauke mu kamar bamu san abinda mu ke yi ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin jawabi ga masu zanga-zanga, babban sakataren jihar na ofishin tsaro, Dr Alfred Mboto ya dora laifin kan gwamnatin tarayya na yadda aka yi watsi da Cross River a bangaren tallafi.

Ya sanar da tsoffin tsagerun cewa gwamnatin jihar ta yi iyakar kokarin ta, ya kara da yin alkawarin za a duba kokensu nan da watan Janairun 2022.

Ya ja kunnensu a kan daukar doka a hannunsu, Daily Trust ta ruwaito.

Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB

A wani labari na daban, Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin kungiyar 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB).

Read also

Bidiyon yadda aka tsinka wa sabon gwamna mari yayin da yake jawabin rantsarwa a Iran

Ya sanar da hakan ne yayin martani kan caccaka mai zafin da wata jaridar London, The Economist ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa.

Jaridar ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta ce mulkinsa ya gaza shawo kan rashawa, Daily Trust ta ruwaito. A wata wallafa ta ranar 23 ga watan Oktoba, mujallar ta baje rundunar sojin Najeriya inda ta ce karfin rundunar a takarda kawai ya ke.

Source: Legit.ng

Online view pixel