Ba zan iya zama da matata ba, tamkar a wuta nake: Magidanci ya roki 'yan sanda su kai shi gidan yari

Ba zan iya zama da matata ba, tamkar a wuta nake: Magidanci ya roki 'yan sanda su kai shi gidan yari

  • Wani magidanci ya kai kansa ofishin yan sanda ya roki a kai shi gidan gyaran hali ya huta
  • Hakan na zuwa ne bayan daurin talala da aka masa a gida saboda laifin safarar kwayoyi
  • Sai dai magidancin ya ce ya gaji da zama da matarsa a gida, ji ya ke tamkar kamar wuta ya ke

Italy - Wani mutum da aka yi wa daurin talala a gidansa a kasar Italiya ya tafi ofishin yan sanda ya nemi a sakaya shi a bayan kanta saboda ba zai iya cigaba da jure rayuwa da matarsa ba a gida.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa yan sandan Carabinieri ne suka bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka fitar.

Mutumin mai shekaru 30 dan kasar Albania da ke zaune a Guidonia Montecelio, kusa da Rome, ya ce 'ba zai iya cigaba da zama da matarsa ba a gida daya,' kamar yadda ya ke a sanarwar.

Read also

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Ba zan iya zama da matata ba, tamkar a wuta nake: Magidanci ya roki 'yan sanda su kai shi gidan yari
Ba zan iya zama da matata ba: Magidanci ya roki 'yan sanda su kai shi gidan yari. Hoto: Guardian NG
Source: Facebook

Sanarwar da yan sandan Carabinieri kusa da Tivoli suka fitar ta ce:

"Ya ga ba zai iya jure lamarin ba, hakan yasa ya tsere, nan take ya kuma kai kansa wurin yan sanda a Carabinieri ya bukaci a sakayya shi a bayan kanta."

Kyaftin Giacomo Ferrante na Tivoli Carabinieri ya ce mutum ya kasance tsare a gida saboda samunsa da laifuka masu alaka da safarar miyagun kwayoyi kuma yana da sauran shekaru kafin a sake shi.

Ferrante ya ce:

"Yana zaune a gida ne tare da matarsa da iyalinsa. Yanzu zaman nasu babu dadi."

Ya ce, ka saurare ni, zama na a gida tamkar wuta na ke, ba zan iya ba, ina son a kai ni gidan yari."

Nan take aka kama mutumin saboda saba hukuncinsa na daurin talala a gida kuma ma'aikatan shari'a sun bada umurnin a kai shi gidan yari.

Read also

Na kashe mutum biyu: Yaro mai shekaru 14 da aka kama cikin 'yan bindiga a Katsina

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani labarin, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel