Na kashe mutum biyu: Yaro mai shekaru 14 da aka kama cikin 'yan bindiga a Katsina

Na kashe mutum biyu: Yaro mai shekaru 14 da aka kama cikin 'yan bindiga a Katsina

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta yi holen wani yaro mai shekara 14 kuma dan bindiga
  • Kakakin yan sandan jihar Katsina Gambo Isah ya ce yaron ya fada musu cewa ya kashe mutane biyu a Mallamawa
  • Yaron da aka sakayya sunansa ya ce ya yi nadamar abubuwan da ya aikata kuma yana fatan ya sauya halayensa

Katsina - Yan sanda a jihar Katsina sun yi holen wani yaro mai shekaru 14 (da aka boye sunansa) da ake zargi dan bindiga ne, Premium Times ta ruwaito.

Da aka holensa tare da wasu mutum 19, kakakin yan sandan jihar, Gambo Isa ya ce yaron ya amsa cewa ya kashe mutane biyu a Mallamawa a karamar hukumar Jibia wasu watanni da suka shude.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya

Na kashe mutum biyu: Yaro mai shekaru 14 da aka kama cikin 'yan bindiga a Katsina
Yaro mai shekaru 14 da aka kama cikin 'yan bindiga a Katsina. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaron, wanda ya ce ya iya amfani da Ak-47, ya ce hatsabibin dan bindiga, mai garkuwa da mutane da kuma barawon shanu, Maliki, ne ya bashi horaswa.

Mr Isa ya ce:

"Yaron ya fada mana cewa an sha zuwa da shi kai hare-hare a kauyyuka a jihar da ma wajen jihar inda ya ce zai iya tuna cewa ya kashe mutane biyu a Mallamawa.
"Ya kuma ce yana cikin wadanda suka kai gari a Dankulumbo da Kukar Babangida duk a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina. Ya kuma ce ya sace dabobi da dama yayin hare-haren da suka kai."

Yayin da aka yi holensa, yaron ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata kuma yana son ya sauya halayensa kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Sace Matafiya 13 a Jihar Neja

An kuma kama masu kwarmatawa yan bindiga bayanai da sayo musu fetur

An kuma yi holen wasu masu kai wa yan bindiga bayanai da hedkwatar yan sandan na Katsina.

Mr Isa ya ce cikin wadanda aka kama akwai wai Samaila Rabiu da aka ce an kama shi da shannu 56 fa jaki daya da akuyoyi uku.

Mutane uku cikin wadanda ake zargin, su kuma an kama su ne kan zargin siyo wa yan bindigan man fetur, saka musu kudi a banki da ciro kudi da sayar da dabobin sata.

Wandanda ake zargin sune Garba Isa, Kabir Garba da Yusuf Garba.

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Kara karanta wannan

Ba zama: Wani mutum ya yi garkuwa da dan sufeton 'yan sanda

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel