Daukar aikin dan sanda: Za'a fitar da sunayen wadanda sukayi nasara a mataki na farko

Daukar aikin dan sanda: Za'a fitar da sunayen wadanda sukayi nasara a mataki na farko

  • Hukumar yan sanda zata cigaba da shirin daukar sabbin jami'ai
  • Hukumar ta bayyana cewa za'a duki sabbin jami'ai 10,000
  • Wadanda sunansu ya bayyana asu zana jarabawa

Abuja - Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da cewa ranar Litinin za ta saki sunayen wadanda suka yi nasara a mataki na farko na neman aikin shiga yan sanda.

Kakakin hukumar, CP Frank Mba, ya bayyana hakan ne a jawabin da saki da ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, 2021.

Zaku tuna cewa hukumar yan sanda na shirin daukan sabbin jami'ai 10,000.

Frank Mba yace:

"Hukumar yan sandan Najeriya tare da gudunmuwar hukumar jin dadin yan sanda asu kammala aikin daukar sabbin yan sanda 10,000 da aka fara a 2020."
"Saboda haka wadanda suka nemi aiki su duba shafin hukumar 'www.policerecruitment.gov.ng' wanda a'a bude ranar Litinin, 18 zuwa Talata 26 ga Oktoba, 2021."

Read also

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

"Wadanda suka samu nasarar ganin hayewa mataki na biyu su fitar da takardar jarabawar saboda ita zasu gabatar ranar jarabawar da aka shirya ranar Juma'a, 29 ga Okotona da Asabar, 30 ga Oktoba a zababbun wurare."

Ya kara da cewa masu neman aiki su duba akwatin email da wayoyinsu kuma su sani cewa kada su biya kowa sisin kobo.

Daukar aikin dan sanda: Za'a fitar da sunayen wadanda sukayi nasara a mataki na farko
Daukar aikin dan sanda: Za'a fitar da sunayen wadanda sukayi nasara a mataki na farko
Source: Facebook

Buhari: Na Bada Umurnin Ɗaukan Sabbin Ƴan Sanda 10,000 da Yi Musu Ƙarin Albashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatinsa a halin yanzu tana aikin daukan sabbin jamian yan sanda 10,000 domin inganta tsaron kasa, Channels ta ruwaito.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis a jihar Legas yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar domin kaddamar da wasu ayyuka.

Read also

Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa

Yace:

"A halin yanzu muna kan daukan sabbin jami'an yan sanda 10,000 domin karfafa tsaro a sassan kasar."

"Na umurci hukumar kula da albashi na kasa ta kara wa yan sanda albashi da alawus-alawus."

Source: Legit.ng

Online view pixel