Buhari: Na Bada Umurnin Ɗaukan Sabbin Ƴan Sanda 10,000 da Yi Musu Ƙarin Albashi
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na kan aikin daukan sabbin yan sanda 10,000
- Buhari ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai jihar Legas a ranar Alhamis domin kaddamar da ayyuka
- Shugaba Buhari ya ce babu wata gwamnati da ta yi wa yan sanda gata kamar nasa tun shekarar 1999
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatinsa a halin yanzu tana aikin daukan sabbin jamian yan sanda 10,000 domin inganta tsaron kasa, The Channels ta ruwaito.
News Digest ta ruwaito cewa Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis a jihar Legas yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar domin kaddamar da wasu ayyuka.
DUBA WANNAN: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi
"A halin yanzu muna kan daukan sabbin jami'an yan sanda 10,000 domin karfafa tsaro a sassan kasar," in ji Buhari.
Ya kara da cewa, "Na umurci hukumar kula da albashi na kasa ta kara wa yan sanda albashi da alawus-alawus."
Kazalika, Shugaba Buhari ya ce tun shekarar 1999 babu wata gwamnati da ta tabuka irin kokarin da gwamnatinsa ta yi wurin kawo sauye-sauye a rundunar yan sanda da tsarin tsaro a kasar.
Bugu da kari, shugaban kasar ya lissafa wasu dokoki da ya rattaba hannu a kai tun hawarsa mulki wadanda suka shafi walwala da jin dadin yan sanda da inganta ayyukansu.
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Buhari ya umurci sojoji su 'bi da ƴan bindiga da salon da suka fi gane wa'
Wasu daga cikinsu sun hada da dokar asusu na musamman na walwala da samarwa yan sanda kayan aiki da ya rattaba hannu a kai a 2019 da kuma yi wa dokar kafa yan sanda kwaskwarima a 2020.
Daga karshe, Buhari ya yabawa gwamnan jihar Legas kan samarwa yan sanda sabbin kayan aiki da zai taimaka musu wurin yaki da bata gari da tabbatar da doka da oda musamman bayan barnar da aka yi musu yayin zanga-zangar EndSARS.
A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.
Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.
Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng