Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50

Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50

  • An kama wasu 'yan Nigeria 11 a Amurka bisa laifuka na almundahar kudade
  • Laifukan da suka aikata sun hada da damfarar kamfanoni da mutane ta hanyar soyayya
  • Masu bincike sun ce za a gurfanar da su a kotu domin su girbi abin da suka shuka

Amurka - Hukumar binciken shari'a na Amurka ya gurfanar da wasu 'yan Nigeria 11 a kotu kan zarginsu da hada baki wurin aikata almundahar kudade, damfara ta banki da satar kudade da sunan wasu.

A ranar Laraba ne Attoni na Kudancin New York, Damian Williams da Jam'in FBI mai kula da New York, Patrick J, Freancy suka sanar da sunayen 'yan Nigeria 11 da ke da hannu wurin karkatar da miliyoyin daloli daga damfarar imel da damfarar soyayya.

Kara karanta wannan

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka gurfanar a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50
'Yan Nigeria 11 da aka gurfanar a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar binciken shari'a na Amurka ta bayyana hakan a ranar Laraba kamar yadda ya zo a ruwayar SaharaReporters.

An kama mutum tara cikinsu a New Jersey da Gabashin New York kuma za a gurfanar da su gaban Mai shari'a Sarah Netburn a Kudanci New York.

Daya daga cikin wadanda ake zargin an kama shi ne a kudancin Texas kuma za a masa shari'a a kotun tarayya na yankin. Daya kuma har yanzu ana nemansa.

Jerin sunayensu

Wadanda ake zargi da almundahar kudin sune:

  1. Adedayo John
  2. Oluwadamilola Akinpelu
  3. Kazeem Raheem
  4. Morakinyo Gbeyide
  5. Warris Adenuga, a.k.a 'Blue'
  6. Smart Agunbiade
  7. Lateef Goloba
  8. Samsondeen Goloba
  9. Olawale Olaniyan
  10. Olawoyin Peter Olarewaju, da
  11. Emmanuel Oronsaye-Ajayi

An ruwaito Williams na cewa:

"Kamar yadda ake tuhumarsu, wadanda aka kama suna cikin wata kungiyar bata gari da ke damfarar kamfanoni a intanet sannan suna damfarar dattawa ta hanyar yaudarar su da soyayya suna tura musu kudade, godiya ga 'yan sandan sirri na Secret Service, yanzu wadanda ake tuhuma suna kotu."

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m

Freaney ya ce 'yan sandan na Secret Service za su cigaba da kare 'yan Amurka daga barazanar 'yan damfara masu yi wa kudadensu barazana kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

‘Yan sanda sun yi ram da wani sojan bogi, mai yi wa mata sata da sunan zai aure su

A wani rahoton, ‘yan sanda sun kama Mkwatula mai shekaru 38 bisa yi wa tarin mata sata bayan dankara mu su karyar shi sojan Malawi ne kuma auren su ze yi bisa ruwayar LIB.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ntcheu, Rabecca Kwisongole ta ce wanda ake zargin ya dade ya na yaudarar mata da soyayya da kuma alkawarin auren su.

A cewar Kwisongole, bayan kwanaki da mika tayin soyayyar sa ga mace, Mkwatula zai lallaba ya sace mu su abubuwa masu daraja kamar babura, talabijin, wayoyi, barguna har kudade ma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel