Neja: Mafarauta Da Ƴan Sa-Kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Harin Kwantar Ɓauna

Neja: Mafarauta Da Ƴan Sa-Kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Harin Kwantar Ɓauna

  • An nemi mafarauta 2 an rasa bayan bata-kashin da ya auku tsakanin farautan, ‘yan sa kai da ‘yan bindiga
  • Lamarin ya auku ne a anguwar Farin Doki da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja ranar Talata
  • ‘Yan sa kai da mafarauta sun yi wa ‘yan bindigan kwanton bauna bayan samun labarin za su kai hari garin

Neja - Mafarauta 2 sun bata bayan sun hada guiwa da ‘yan sa kai wurin halaka ‘yan bindiga da dama a anguwar Farin Doka dake karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

The Punch ta ruwaito yadda lamarin ya auku a ranar Talata bayan ‘yan bindiga sun afka wa yankin.

Neja: Mafarauta Da Ƴan Sa-Kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Harin Kwantar Ɓauna
Taswirar Jihar Neja. Hoto: Channels TV
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa:

“Yan bindigan da yawan su a kan babura sun shiga wasu kauyaku da ke wuraren anguwar Farin Doki. Ba su san ‘yan sa kai da mafarauta sun yi mu su kwanton bauna ba bayan samun labarin za su kai farmaki yankin.”
“Dama gwamnati ta datse hanyar sadarwa tsakanin ‘yan bindiga da ma su kai mu su labaran sirri ta hanyar datse kafafen sadarwa a anguwannin don taimako wurin shawo kan rashin tsaro.”

Wakilin Punch ya tattara bayanai akan yadda bayan sa’o’i 2 da kammala musayar wuta tsakanin ‘yan sa kai da su ka hada kai da mafarauta wurin ragargazar ‘yan bindiga, an samu nasarar halaka ‘yan bindiga da dama bayan sun datsi ‘yan sa kai 2 inda su ka mutu har lahira da makaman su.

An kwace babura da makamai a hannun su

Kamar yadda Punch ta ruwaito, majiyar ta bayyana cewa:

“An samu nasarar amsar babura, bindigogi kirar AK-47 da makamai da dama daga hannun ‘yan bindigan. ‘Yan bindiga yanzu sun hada guiwa da ‘yan Boko Haram wurin horar da matasan yankin.”

Read also

‘Yan bindiga sun sace tagwayen ‘yan mata, Direba da wasu Dogaran Sarki a Najeriya

An samu bayanai akan yadda jami’an tsaro su ka kama fiye da mutane 22 da ake zargin su na da alaka da ‘yan bindiga a anguwannin guda 4 bayan an bi maboyar su.

Cikin wadanda ake zargin akwai wadanda aka kama da makamai, kuma an wuce da su ofishin jami’an tsaro da ke Zumba, daga nan za a wuce da su hedkwatar ‘yan sanda dake Minna, babban birnin jihar.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, ASP Wasiu Biodun ya yi alkawarin yin bincike dangane da abinda ya faru tsakanin ‘yan bindigan da mazauna yankin kuma idan ya yi hakan zai sanar da wakilin Punch idan ya kammala binciken.

Har yanzu dai ba a ji komai ba, daga wurin shi.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Read also

Babban malamin addini ya goyi bayan Gumi, ya goyi bayan a yi wa tubabbun ƴan Boko Haram da ƴan bindiga afuwa

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Source: Legit.ng

Online view pixel