Babban malamin addini ya goyi bayan Gumi, ya goyi bayan a yi wa tubabbun ƴan Boko Haram da ƴan bindiga afuwa
- Babban Faston cocin Methodist, Dr. Samuel Chukwuemeka Kanu-Uche, ya bayar da goyon baya dangane da yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga
- Kanu-Uche ya ce hakan daya daga cikin hanyoyin samar da zaman lafiya ne a cikin kasar nan kamar yadda ya sanar da manema labarai a Abuja
- A cewar sa ya yi matukar farin cikin jin malamai musulmai su na cewa Qur’ani ma be yarda da kashe-kashen rayukan jama’a ba kamar yadda Bible ma ya nuna
Abuja - Babban faston cocin Methodist Church Najeriya, Dr. Samuel Chukwuemeka Kanu-Uche, ya goyi bayan yafe wa tubabbun ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram don samar da zaman lafiya a kasa.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa zaman lafiya ba rashin matsaloli bane, face salo da dabarar kawo karshen matsaloli don kada a samu barkewar tashin hankali.
Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen
A cewar sa Najeriya ta fara samun matsaloli ne tun bayan mutane sun fara mayar da lamarin addini, duk da addini hadin kai yake sanya wa ba ya lalata alakar jama’a ba.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, faston ya bayyana cewa:
“Na yi farin ciki da na ji malaman musulunci su na cewa Qur’ani be bayar da umarnin a kashe rayuka ba. Ya bayar da damar kare kai, matsawar aka takura ka sai ka kare kan ka kamar yadda aka umarci kiristoci, mu na kiran shi da salon Nehemiah. Sai har an kai ka bango, ba ka je ka dauki doka a hannun ka ba balle ka cutar da wanda be ji ba be gani ba.”
Faston ya bukaci a dinga bai wa Sheikh Gumi kwarin gwiwa
Yayin da yake amsa tambayoyi akan Boko Haram da ‘yan bindiga, malamin ya bukaci a kara wa Sheikh Gumi kwarin guiwa don samar da mafita maimakon a dinga caccakar sa.
Kanu-Uche ya ce:
“Idan ba ku fatattake shi ba kun ce shi mutumin banza ba ne, zai iya shiga daji wurin ‘yan bindiga daga nan gwamnati za ta iya amfani da shi a matsayin kafar tattaunawa da su.”
“Idan gwamnati za ta yanke shawarar biyan ‘yan bindiga N25,000 duk wata, ya fi akan su ci gaba da garkuwa da mutane. Abinci suke bukata.”
Dangane da yafe wa ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga ya bayyana cewa:
“Ina goyon bayan a yafe mu su, kamar yadda aka yafe wa ‘yan yankin Niger Delta, wanda aka zaunar dasu a ka gusar mu su da kishin man fetur.”
“Ya kamata gwamnati ta yafe wa Nnamdi Kanu, Sunday Adeyemo wato Sunday Igboho da sauran su. Za a iya zama da su don tattauanawa da su. Idan ana bukatar zama da kiristocin kudu maso gabas, a gayyace ni.”
“A zauna da mutane kamar Chief (Emmanuel) Iwuanyanwu, don su san an sanya manyan malaman kiristoci kuma kada a kira su da ‘yan ta’adda. Idan aka kira su da ‘yan ta’adda za a kawo gaba tsakanin su da yaran mu kuma za a fi zama da su cikin kwanciyar hankali.”
Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa
A wani labarin, kun ji cewa Ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun fara tambayar dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa, rahoton Daily Trust.
Ƴan bindigan sun janye kai hare-hare a garuruwa tun bayan da gwamnatin jihar ta soke cin kasuwannin mako-mako don daƙile rashin tsaro.
Wani shugaban matasa a ɗaya daga cikin ƙauyukan Birnin Gwari, Babangida Yaro ya shaidawa Daily Trust cewa tun bayan hana cin kasuwanni ƴan bindiga da ke sace mutane a ƙauyukan Kutemashi da Kuyello dafaffen abinci suke tambaya duk lokacin da suka sace mutane.
Asali: Legit.ng