‘Yan bindiga sun sace tagwayen ‘yan mata, Direba da wasu Dogaran Sarki a Najeriya

‘Yan bindiga sun sace tagwayen ‘yan mata, Direba da wasu Dogaran Sarki a Najeriya

  • Ana zargin ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘ya ‘yan Sarkin Obbo Ayegunle
  • An dauke ‘Ya ‘ya, Dogari, Direba da wata Hadimar Mai martaba a titin Osi
  • Jami’an ‘Yan Sandan jihar Kwara sun tabbatar da aukuwar wannan lamari

Kwara - Tagwayen ‘ya ‘ya matan Mai martaba Owalobo na kasar Obbo Ayegunle a karamar hukumar Ekiti, jihar Kwara sun fada hannun ‘yan bindiga.

Rahoto daga jaridar Daily Trust ya tabbatar da cewa an sace ‘ya ‘yan mai martaban ne tare da wasu dogaran fada a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021.

Wannan lamari ya auku da kimanin karfe 6:30 a daren Juma’a. ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wadannan Bayin Allah a kan hanyar dawo wa Obo Ayegunle.

Wata majiya tace ‘ya ‘yan Mai martaban da fadawan na sa suna dawo wa ne daga garin Osi a jihar Kwara. Tagwayen 'ya 'yan sarkin ba su wuce shekaru shida ba.

Read also

Neja: Mafarauta Da Ƴan Sa-Kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Harin Kwantar Ɓauna

Jerin wadanda miyagu suka yi gaba da su

Miyagun ‘yan bindigan sun hada har da direban Sarkin na Obbo Ayegunle, wanda aka bada sunansa da Kunle, da wani jami’in tsaronsa, Lawrence Abiodun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan bindiga
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Baya ga ‘ya ‘yan na sa, ‘yan bindigan sun yi awon-gaba da wata hadimar Sarki mai suna Bukunmi Akanbi. Har zuwa yanzu ba a ji labarin halin da suke ciki ba.

Kawo yanzu da ake tattara rahoton, ba a ji labarin an tuntubi Sarki ko wani a cikin ‘yan uwansa a kan a biya kudin fansa kafin a saki wadanda aka dauken ba.

An bar motar Mai martaba wanda aka yi mata shaida da “Owalobo of Obbo Ayegunle” a lamba a kan titi, yayin da ‘yan bindigan suka tsere da wadannan mutane.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, yace za su hada-kai da sauran jami’an tsaro domin a ceto duk wadanda suke tsare.

Read also

Rashin tsaro: Sojoji sun samu gagarumar nasara, sun hallaka ‘Yan bindiga rututu a kwana 13

Ajayi Okasanmi ya bayyana cewa dakarun ‘yan sanda za su yi aiki da sauran ‘yan bangan da ke yankin da nufin kubuto da na-kusa da Sarkin daga ‘yan bindiga.

An kashe 'Yan bindiga a Sokoto da Kaduna

A karshen makon nan ne ku ka ji hedikwatar tsaro ta kasa ta bada albishir, tace sojojin kasa da na sama sun aika ‘Yan bindiga rututu zuwa barzahu a Birnin Gwari.

Jami’an tsaro sun kashe miyagun ‘yan bindiga sama da 40 tsakanin farkon Oktoba zuwa yanzu. Dakarun kasar sun samu wannan nasara ne a Sokoto da Kaduna.

Source: Legit

Online view pixel