Tarihin Gwamnan Najeriya da Ya Sha Azaba Yana Talla kafin Samun Arziki
- Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana yadda rasuwar mahaifinsa ta tilasta masa fita yin talla a titunan Legas domin tallafa wa mahaifiyarsa
- Ya ce wahalhalun da ya sha tun yana dalibi ne suka gina masa ruhin kasuwanci da jajircewa da suka kai shi kololuwar nasara a yanzu
- Gwamnan ya gargadi matasa kan son samun nasara cikin gaggawa ba tare da aiki tukuru ba, yana kira gare su su rungumi aiki sosai da gaskiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun – Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya ba da labarin wani bangare na rayuwarsa mai cike da kalubale, inda ya bayyana cewa rasuwar mahaifinsa ta tilasta masa fita yin talla a titunan Legas domin taimakawa 'yan uwansa.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin gabatar da jawabin taron kammala karatu karo na bakwai a Jami’ar Mountain Top da ke Ibafo, a jihar Ogun.

Source: Facebook
Punch ta rahoto ya ce rasuwar mahaifinsa, wanda dan sanda ne da ya rasu yana bakin aiki, ta sauya akalar rayuwarsa tun yana saurayi, lamarin da ya sa rayuwa ta yi tsanani gare su.
Yadda Gwamna Umo Eno ya yi talla
Umo Eno ya ce bayan mutuwar mahaifinsa, wahalar ayuwa ta karu matuka, inda ya zama dole ya taimaka wa mahaifiyarsa wajen kara samun kudin shiga.
Ya bayyana cewa yana fita yin tallan lemun kwalba a titunan Legas duk da kasancewarsa daya daga cikin shugabannin dalibai a makarantar sakandare ta Victory High School.
Gwamnan ya ce wannan lokaci ne da ya koya masa darussan hakuri, aiki tukuru da dogaro da kai, yana mai cewa abubuwan da ya fuskanta sun taimaka masa wajen koyon dabarun kasuwanci da hangen nesa.

Source: Twitter
Ya bayyana wadannan kalubale a matsayin tubalin da ya gina rayuwarsa, wanda daga bisani ya kai shi ga kafawa da tafiyar da manyan kamfanonin lura da baki da yawon shakatawa a jihar Akwa Ibom.
Sakon Gwamna Eno ga dalibai
A jawabinsa, gwamnan ya bukaci dalibai da su zama masu fatan cin nasara, su kuma yi aiki tukuru domin cimma burinsu. Ya gargade su kan tunanin cewa nasara na zuwa ba tare da wahala ba.
Umo Eno ya ce a yau duniya ta sauya salo sakamakon cigaban fasaha da aka samu, lamarin da ke bukatar tunani mai kyau da jarumta wajen fuskantar zaman duniya.
A sakon da ya wallafa a X, gwamnan ya bayyana cewa da yawa daga cikin matasan zamani na fama da tunanin samun nasara cikin gaggawa, yana mai cewa irin wannan tunani kan jawo nadama.
Gwamnan Akwa Ibom ya yi kyautar N100m
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamna Umo Eno ya yi kyautar kudi har Naira miliyan 100 ga wani mai wakar yabo.
Gwamna Eno ya bayyana cewa kudin za su iya gina masa gida mai dakuna da dama da zai zauna ya samu shagon sana'a.
A bayanin da ya yi, ya ce ya bayar da kyautar ne ga mutumin da ya rungumi wakokin yabo duk da cewa shi makaho ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


