Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Titunan Legas, Bidiyon Barnar da Ruwan Ya Yi Ya Ja Hankali

Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Titunan Legas, Bidiyon Barnar da Ruwan Ya Yi Ya Ja Hankali

  • Mazauna karamar hukumar Alimosho ta jihar Legas sun yi cirko-cirko a kan tituna biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya janyo ambaliya
  • Ruwan saman ya sauka ne tsakanin karfe biyu na dare zuwa a wasu yankuna na jihar ya ci gaba da sauka har zuwa karfe 10 na safiya
  • An gargadi wadanda ke zaune a yankin 'Command' din Alimosho da su kauracewa bi ta kan 'gadar Command' saboda ruwan ya mamaye ta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Mazauna yankin 'Command' a karamar hukumar Alimosho ta jihar Legas sun yi cirko-cirko tare da motocinsu, yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye babbar gadar yankin a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Hotuna da bidiyo, kamar yadda Legit.ng ke gani, sun nuna yadda mazauna yankin ke kokarin bi ta hanyar da ambaliyar ruwa ta mamaye a kokarin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Legas
Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Legas, mutane sun yi cirko-cirko. Hoto: NEMA Nigeria
Asali: Twitter

A cewar Vanguard, jami’in hulda da jama’a na hukumar NEMA a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da cewa ana kokarin ceto wadanda ambaliyar ta rutsa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sahara Reporters, Farinloye ya ce:

“An yi kira ga mazauna yankin 'Command' da su bi wasu hanyoyin daban domin gujewa gadar 'Command' saboda ambaliya ta mamaye gadar.

Hukumar NEMA, hukumar kashe gobara da ‘yan sanda suna aiki don fitar da mutanen da suka makale daga yankin a halin yanzu.”

Shawarar NEMA ga mutanen Legas

A halin yanzu, shafin X na NEMA, kamar yadda Legit.ng ta gani, ya rubuta cewa:

Kara karanta wannan

Kasar Girka ta kuduri aniyar halatta auren jinsi, da daukar rainon yara

“Ana kira ga mazauna Legas da su yi taka-tsan-tsan a yayin amfani amfani da wasu hanyoyi na jihar yayin da ambaliyar ruwa ta ke ta'azzara saboda yawan ruwan sama.
"NEMA, hukumar kashe gobara ta LASEMA, 'yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki don fitar da mutane daga wuraren da abin ya fi ta'azzara."

Bayan shafe makwanni ana zafafa zafi, a karshe mazauna Legas sun samu sauki yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata.

Legas: Hatsari mota ya lakume rayukan mutane da dama

A safiyar yau Legit Hausa ta ruwaito cewa wani mummunan hatsarin mota a hanyar Legas zuwa Abeokuta ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 9.

Hukumar kiyaye hadurra ta jihar Ogun ta ce mutum 17 ne hatsarin ya rutsa da su, amma 9 sun mutu yayin da bakwai suka jikkata.

An ruwaito cewa hatsarin ya afku ne sakamakon gudun wuce sa a da motocin ke yi akan babbar hanyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel