Kimiyya da fasaha: An ƙera wata motar ‘Tasi’ mai a sararin samaniya
Sakamakon yawaitan cunkoson ababen hawa a titunan kasar Dubai, masana ilimin kimiyya sun samar da wata karamar mota, kirar tasi mai tashi sama don rage matsalar cunkoso a kasar.
Shi dai wannan mota mai suna ‘Volocopter’ an fara gwajin shi ne a kasar Jamus, kuma yana tashi da sauka kamar jirgin sama mai tashin angulu, kuma zai dinga daukan fasinjoji guda biyu ne a lokaci daya.
KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: ýan bindiga sun kai hari hedikwatar EFCC, sun bar ma wani jami’in hukumar saƙo
Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar za’a samar matukin motar guda daya, sa’annan kuma za’a iya barinsa ya tuka kansa da kansa, kamar yadda daraktan hukumar kula da ababen hawa na kasar Dubai, Mattar Al-Tayer ya bayyana.
Sai dai matsalolin da ake fuskanta dangane da motar shine, hankulan matuka jirgin sama bai kwanta da wannan cigaban ba, inda majiyar Legit.ng ta ruwaito wani matukin jirgin Markus Wahl yana fadin:
“ba zan taba shiga wannan motar ba, saboda matsalar wuta, wanda ka iya cutar da fasinja.”
Fitaccen kamfanin nan daya shahara wajen kera jiragen sama, Airbus, shima ya shiga tsarin kera irin wannan mota, inda a yanzu haka suna kera motar tasi mai tashi sama kuma ba tare da direba ba, burinsu su samar da motar da fasinja zai iya sarrafa tat a hanyar amfani da wayar salula.
Bincike ya tabbatar da babban matsalar da ake fuskanta da ire iren wadannan motoci shine matsalar batir, batiransu basa wuce mintuna 30 suke mutuwa. Duk da haka ana sa ran zuwa shekarar 2030 za’a fara amfani da wannan mota a Dubai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng