Yadda Mutuwar Dan Ta'adda Halilu Sububu Za Ta Takaita Ayyukan Ta'addanci a Arewa
- Halilu Sububu, hatsabibin dan bindiga ne wanda ya yi kaurin suna a kai hare-hare a garuruwan yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- An ce Sububu ya tara dukiya mai yawa daga safarar makamai, garkuwa da mutane, alakarsa da 'yan jihadin Sahel da hakar ma'adanai
- Bayan kashe Halilu Sububu a ranar Alhamis, tambaya daya ke yawo a zukatan jama'a; shin yanzu ta'addanci zai ragu a Arewacin Najeriya?
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Hamshakin attajirin dan bindiga Halilu Sububu da ke da alaka mai zurfi da masu jihadi na yankin Sahel, ya wuce a kira sa dan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Mulkinsa na ta’addanci ya zo karshe da yammacin ranar Alhamis bayan da jami’an tsaro da ‘yan banga suka kashe shi a wani artabu da kungiyarsa a jihar Zamfara.
Ayyukan ta'addancin Halilu Sububu
Tsokacin da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa Sububu na daga cikin ‘yan bindiga na farko farko da suka dauki makami a shekarar 2011.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Sububu ya dauki bindiga ne domin yakar hare-haren kin jini da ya yi ikirarin wasu a Zamfara na kai wa Fulani a jihar.
Ya horar da wasu fitattun ‘yan ta’adda da suka hada da Shehu Rekep, fitaccen dan ta’addan kuma mai safarar makamai da ya addabar al’ummar Zamfara da Sakkwato.
Ana zargin Sububu ne ya shirya sace daliban kwalejin aikin gona da kimiyar dabbobi ta Zamfara da ke Bakura da wasu mutane 80 a kauyen Gora da ke Maradun ta jihar.
Hannun Sububu sace daliban Kuriga
Ya kuma shiga cikin 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da dalibai sama da 130 a Kuriga, jihar Kaduna.
Wani shugaban ‘yan bindiga, Yellow Janbros ne ya yi garkuwa da daliban, amma saboda bai kware a harkar ba sai ya ba Dogo Gide kwangilar yakar jami’an soji da ke bibiyar tawagarsa.
An ce shi Janbros ya kuma kai wasu daga cikin daliban zuwa sansanin Sububu da ke jejin Bawar Daji a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Dukiya daga safarar makamai
An rahoto cewa Sububu na daya daga cikin ‘yan ta’adda mafiya arziki a Arewacin Najeriya. Ya kasance babban mai safarar makamai kuma mai horar da amfani da makaman.
Shehu Rekep, mataimakinsa ya na da dangantaka mai karfi da kungiyoyin 'yan tawaye a Mali, Chadi, da Libya, wanda ya taimakawa Sububu a sana'arsa ta safarar makamai.
Amma ana kyautata zaton harkallar makamai ta Sububu ta bazu zuwa wasu kasashe da suka hada da Burkina Faso, Morocco, Algeria, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Senegal.
Alakar Sububu da 'yan ta'addar Sahel
Baya ga sana’arsa ta safarar makamai, Sububu da ‘yan kungiyarsa sun kuma kai hare-hare a sansanin soji da al’ummomin Arewa, inda suka sace mutane da kame shanu.
Wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa ‘yan fashi irin su Sububu na da alaka da kungiyoyin jihadi masu magana da harshen Faransanci a yankin Sahel.
Sububu ya kuma shiga harkar hakar zinaretare da tilastawa mazauna Bagega da sauran garuruwan da ke kewaye da dajin Sumke a Anka ta Zamfara yin aikin hakar.
Duk wadannan; safarar makamai, hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba da kuma harkar garkuwa da mutane sun sa Sububu ya tara haramtacciyar dukiya mai yawa.
Yadda jami'ai suka kashe Sububu
Majiyoyin cikin gida da ke da masaniya kan motsin Sububu a ranar 13 ga Satumba sun tabbatar da cewa an kashe shi tare da wasu mayakansa a hanyar Mayanchi zuwa Anka.
Yahuza Getso, kwararre kan harkokin tsaro da ke nazarin ayyukan ‘yan bindiga da yadda suke aiki a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya yi karin bayani kan lamarin.
"An kashe shi a ranar Alhamis yayin da ya ke dawowa daga Fakai domin ganawa da Bello Turji. Ana kyautata zaton dan bindiga Saidu a Bayan Ruwa ne ya kai kwarmatonsa.
"Saidu na fargabar Sububu zai kwace wuraren hakar ma'adanar na Maru, musamman a Jabaka da Kuzawa, wannan ta sa ya sanar da jami'an tsaro inda ya ke aka kashe shi."
- A cewar Getso.
Mutuwarsa za ta rage ta'addanci?
Ba Sububu ne dan ta'adda na farko da aka kashe a fafatawar da aka yi da sojojin Najeriya ko kuma kungiyoyin da ke gaba da juna ba.
Ya shiga rukunin wasu 'yan ta'addan da aka kashe kamar su Kachala Ali, Sani Dangote, Damina, Baleri da Modi-Modi, da dai sauransu.
Duk da haka, mutuwarsa za ta iya rage yawan ta'addanci a yankunan Arewa saboda shi ne babban mai safarar makamai ga kungiyoyin ta'addanci masu tasowa.
Amma kuma masana sun damu cewa kungiyarsa za ta iya sake addabar Arewa idan har ba a kawar da manyan kwamandojinsa ba.
Masana harkokin tsaro sun kuma bukaci gwamnati da ta tsaurara matakan tsaro a kewayen iyakokin Najeriya domin dakile kwararowar kungiyoyin 'yan bindiga daga kasashen Sahel.
Kisan Sububu: Sakon Tinubu ga sojoji
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin cikinsa kan nasarar da dakarun sojoji suka samu na halaka dan ta'adda Halilu Sububu.
Shugaban kasar ya ba jami'an tsaro tabbacin ci gaba da ba su goyon baya a kokarin da suke yi na samar da tsaro a fadin kasar nan musamman a Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng