Rekeb, gagararren dan bindiga ya sanar da dalilinsu na yunkurin kafa sansani a Sabon Birni
- Shehu Rekeb, daya daga ciikin gagararrun 'yan bindigan Zamfara ya ce yaran Turji ne suka kai farmaki sansanin soji
- A cewarsa, Turji ya ji labarin cewa dakarun Nijar za su fara taimakon Najeriya, shi ya tura yara suka je domin hana hakan
- A sakon Turji ga shugaba Bazoum na Nijar, ya ce ya fita daga al'amarin da ya kwatanta da na cikin gida, ko kuma za su addabe shi
Sabon Birni, Sokoto - Wasu 'yan bindiga da ke jihar Zamfara an gano cewa suna garzayawa yankin Sabon Birni da ke jihar Sokoto domin suna tsammanin zuwan dakarun sojin Nijar da ke kokarin taimakon Najeriya wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga.
Wani shugaban 'yan bindiga ya ce suna kokarin kafar sansani a kauyukan Ballazu da Gangara na yankin, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sabon Birni karamar hukuma ce da ke tsakanin iyakokin Nijar da wasu kauyuka da ke kan iyaka.
An dinga samun farmakin miyagu a Sabon Birni da kananan hukumomi masu makwabtaka a cikin kwanakin nan inda har suka hada da sansanin soji da ke Burkusuma ina a kalla jami'ai 15 suka rasa rayukansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyoyi kusa da Daily Trust sun sanar da cewa, yaran shugaban 'yan bindiga Turji tare da wasu yaran Halilu Sububu ne suka kaddamar da hare-haren. Su na kuma kai farmaki sau da yawa a Zurmi da Shinkafi ne da ke da kusancin da Sabon Birni.
A yayin karin bayani, Shehu Rekeb, daya daga cikin gagararrun 'yan bindigan ya ce su ne suka kai farmaki kan sansanin sojin ba mayakan ISWAP.
Rekeb ya ce wasu daga cikin jami'an tsaron da suka sace har yanzu suna hannun 'yan bindigar.
Ya ce Turji ne ya jagoranci mutanensa domin kaddamar da hari da fatan kwace yankin domin guje wa sojojin Nijar da yace suna kokarin shigowa kawo wa takwarorin su na Najeriya dauki.
"An ce Nijar za ta zo kawowa Najeriya dauki, hakan yasa muka ce yaranmu su je domin ganin hakan ba ta faru ba," yace.
Ya bukaci shugaban kasan Nijar, Mahamed Bazoum da ya fita daga wannan lamarin da ya kwatanta da na cikin gida, inda ya ce zai fara tura yaransa su kai masa farmaki har Nijar.
Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, Dave Umahi, ya ce sun gano cewa an kaddamar da yaki kan yankinsu a yayin da ya ke martani kan kashe-kashen da 'yan bindiga ke wa jama'arsu.
Kamar yadda Leadership ta ruwaito, Gwamna Umahi ya nuna damuwarsa da alhini kan kisan rayuka 12 da aka yi a yankin a makon da ya gabata kuma ya ce babu gaira balle dalili.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar tsaro na jihar a ofishin sabon gwamnan Abakaliki. Ya zargi wasu Ndigbo da ke zama a kasashen ketare da shirya rigingimun tare da daukar nauyinsu.
Asali: Legit.ng