Mawakin Najeriya Ya Saka Matarsa a Caca, Zai Sake Ta Idan Trump Ya Zama Shugaban Amurka
- Fitaccen mawakin Najeriya Charly Boy ya saka matarsa a caca gabanin gudanar da zaben shugaban kasar Amurka
- Charly Boy ya sha alwashin sakin matarsa wadda suka shafe shekaru 47 suna tare ma damar Kamala Harris ba ta ci zabe ba
- A cewar Charly Boy, Amurka ta cancanci samun shugabar kasa mace ta farko kuma bakar fata bayan Barrack Obama
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Shahararren mawakin Najeriya, Charly Boy wanda ya saba jawo surutu a shafukan sada zumunta da kalamansa, ya sake tayar da hanzo a ranar Litinin.
Charly Boy ya sha alwashin sakin matarsa, da suka shafe shekaru 47 suna zaman aure ma damar hasashensa kan zaben shugaban Amurka bai tabbata ba.
Charly Boy ya magantu kan zaben Amurka
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Charly Boy ya idan har 'yar takarar shugaban kasa, Kamala Harris ba ta ci zabe ba, to ba kamawa sai matarsa ta koma gidansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Charly Boy wanda ya kira mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris da "abar kaunata" ya ce Amurka ta cancanci samun shugabar kasa mace ta farko kuma bakar fata.
A cewar mawakin, tun da kasar ta samu bakin fata (Barrack Obama) to ya kyautu yanzu ma a ce sun samu mace bakar fata domin shugabantar kasar.
Charly Boy ya sha alwashin sakin matarsa
A cewar Charly Boy:
"Idan abar kaunata, Kamala Harris ba ta ci zaben shugabancin Amurka ba. Na rantse, sai na saki matata da muka shafe shekara 47 a tare.
"Bayan shugaban kasa bakar fata na farko, Amurka ta cancanci samun shugabar kasa mace kuma bakar fata ta farko."
Joe Biden ya yafe tazarce a Amurka
Rahotanni sun bayyana cewa, Joe Biden ne ya janye daga neman tazarce, inda kuma ya nada Kamala Harris matsayin wadda za ta yi takara shugabancin kasar a madadinsa.
Shugaba Biden yana sa rai mataimakiyarsa za ta doke Donald Trump a zaben wannan karo.
Duba bayaninsa a kasa:
Jarumi Suleiman Alaka ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Suleiman Alaka rasuwa a ranar Litinin, 22 ga watan Yulin 2024.
Darakta kuma jarumi a masana'antar da ake ji da ita, Al-Amin Ciroma ne ya fitar da labarin sanarwar rasuwar Suleiman inda 'yan Kannywood suka yi ta'aziyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng