Allah wadan naka ya lalace: 'Yar gidan Charley Boy ta wallafa hotunan da ta dauka da abokiyar madigonta

Allah wadan naka ya lalace: 'Yar gidan Charley Boy ta wallafa hotunan da ta dauka da abokiyar madigonta

- 'Yar gidan Charley Boy, ta wallafa hotunan da ta dauka da abokiyar madigonta, kuma masoyiyarta a shafinta na Instagram

- Ta wallafa hotunan ne a shafinta cikin rashin kunya da tsoron maganar mutane

- Su dai wadannan masoya sunyi suna sosai a bangaren bayyana akidarsu ta madigo, infa suke sanya hotunan su a duk lokacin da suka ga dama

'Yar gidan Charley Boy, Dewy Oputa da abokiyar madigonta, SJ sun fara fara daukar wasu hotuna na soyayya a yayin da suka fara murnanr rayuwarsu ta soyayya.

Masoyan wadanda suke zaune a birnin Atlanta sun kasance marasa tsoro nuna akidarsu ta madigo, inda suke bayyanawa duniya irin soyayyar da suke yi da junansu ba tare da kunya ko tsoro ba.

KU KARANTA: 'Yar gidan mataimakin shugaban kasa Kiki Osinbajo ta yi wata muhimmiyar magana game da rayuwar

Ana ta faman samun irin wannan lamari na 'yan madigo dai a shafukan sada zumunta kwanan nan, inda a makon da ya gabata muka kawo muku rahoton yadda, wata budurwar ta kashe kanta saboda abokiyar madigonta ta mutu.

Budurwar dai ta hau kan wata gada ne ta fado saboda ta kasa jure rabuwar ta da abokiyar iskancin na ta.

Haka kuma a daya bangaren mun kawo muku labarin yadda fitaccen dan daudun nan na jihar Legas ya gargadi talakawa da suke aika masa da sakon soyayya ya ce su guji yi masa irin wannan sakonni domin bai zama dan daudu saboda su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng