G Fresh Ya Yi Martani Kan Bankaɗar da Sadiya Haruna Ta Yi, Ya Saki Manyan Maganganu

G Fresh Ya Yi Martani Kan Bankaɗar da Sadiya Haruna Ta Yi, Ya Saki Manyan Maganganu

  • Al'ameen G-Fresh ya yi martani kan maganganun da Sadiya Haruna ta yi inda ta bankada sirrin aurensu baki daya
  • G-Fresh ya karyata dukkan maganganun da Sadiya Haruna ta yi inda ya ce ba zai lamunci matarsa tana harka da kawalai ba
  • Fitaccen dan TikTok din ya bayyana yadda ya durkusa har kasa yana ba ta hakuri domin gyara lamarin amma ya ci tura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen dan TikTok a Najeriya, Al'ameen G-Fresh ya yi martani game da banakadar da Sadiya Haruna ta yi a makon jiya kan aurensu.

G-Fresh ya karyata abubuwa da dama da Sadiya ta fada inda ya ce sun dade su na harka tun kafin su yi aure.

Kara karanta wannan

Alkali ya yi barazanar daure Hadimin Gwamna Abba kan shari'ar Ganduje

G-Fresh ya ƙaryata duka maganganun Sadiya Haruna kan aurensu
Al'ameen G-Fresh ya fayyace gaskiya kan dambarwar aurensa da Sadiya Haruna. Hoto: @G Fresh alameen.
Asali: TikTok

Sadiya Haruna: G-Fresh ya maida martani

G-Fresh ya bayyana haka ne a cikin shirin Gabon's Room Talk Show a faifan biyidon Youtube.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata duk abin da mutum zai fada ya yi gaskiya inda ya ce shi ya ba da kudin haya dole ya tare ba kamar yadda ta ce ita ta biya komai ba.

"Ta yaya mai mata zai yadda matarsa tana harka da kawalai kuma ya yi shiru, ni ban son takurawa mace amma ina da son wacce za mu samu nasara mu inganta rayuwa tare a rayuwa."
"Matsalar aurenmu ta fara ne daga wani figaggen kawalinta, muna zaman lafiya bayan mun fita sai naga ta kai masa wafta, sai na kawar da kai kuma da aurenta."
"Kuma har kwana a gidan yake yi, kafin auren da kuma bayan auren, daga bisani ta fara nuna ya fini muhimmanci a gidan."

Kara karanta wannan

2027: Gwamna ya yi magana kan rade-radin daukarsa mataimakin Atiku a zabe

- Al'ameen G-Fresh

Yadda G-Fresh ya taimaki Sadiya Haruna

G-Fresh ya ce ya samu matarsa suna cin abinci tare inda ya nuna bacin ransa madadin ta bashi hakuri sai ta nuna ta ranta ya zage-zage.

Ya ce ya yi iya bakin kokarinsa wurin bata hakuri amma taki inda take kora masa munanan ashariya har da iyayensa.

Har ila yau, G-Fresh ya karyata zancen cewa shi yaron Sadiya ne inda ya ce har taimakonta yake yi wurin daurata a layin neman kudi.

Kalli cikakken hirar a nan:

Sadiya Haruna ta caccaki G-Fresh kan aurensu

Kun ji cewa Sayyada Sadiya Haruna ta bankada sirrin aurensu da Al'ameen G-Fresh inda ta fadi yadda suka fara haduwa.

Sadiya Haruna ta ce G-Fresh yaronta ne inda ta ce ba ta taba tsammanin ko da kudi za ta iya aurensa ba a rayuwarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.