A karo Na 7, Sayyada Sadiya Haruna, Tsohuwar Matar G Fresh Zata Amarce

A karo Na 7, Sayyada Sadiya Haruna, Tsohuwar Matar G Fresh Zata Amarce

  • A yau Juma'a ne za a daura auren fitacciyar jarumar TikTok, Sayyada Sadiya Haruna, tsohuwar matar G-Fresh Al'amin
  • Ita da kanta Sadiya Haruna ta wallafa katin daurin auren mai dauke da sunan angon da za ta aura, Hon. Babagana Audu Grema
  • Wannan ne karo na bakwai da za ta yi aure kamar yadda ta sanar a zauren hirar da tayi da Hadiza Gabon, fitacciyar jarumar Kannywood

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - A yau Juma'a, 5 ga Yulin 2024, fitacciyar jarumar TikTok kuma mai siyar da kayan mata, Sayyada Sadiya Haruna za ta yi aure karo na bakwai.

Sadiya Haruna ta dora katin gayyatar zuwa daurin aurenta, wanda za a yi a Maiduguri dake jihar Borno.

Kara karanta wannan

Jihar Adada: Muhimman abubuwa 5 game da shirin kirkirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas

Sayyada Sadiya Haruna za ta amarce a karo na 7
Sayyada Sadiya Haruna, tsohuwar matar G-Fresh za ta sake yin wani auren karo na 7. Hoto: Sayyada Sadiya Haruna
Asali: Facebook

Sadiya ta wallafa katin aurenta da sabon angonta mai suna Honarabul Babagana Audu Grema a shafinta na TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan yana zuwa jim kadan bayan kashe aurenta da shahararren dan TikTok, G-Fresh Al-Amin.

Rabuwar auren Sadiya da G-Fresh

Wannan dai na zuwa ne 'yan watanni bayan kashe aurenta da fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al-Ameen, wanda ya jawo cece kuce a intanet.

A halin yanzu takaddama kala-kala ce ta dabaibaye dalilin rabuwar su tun bayan da kotun addinin Musulunci ta shiga tsakaninsu.

Sayyada Sadiya Haruna ta sanar da cewa, ta biya shi kudi har N500,000 domin ta fanshi kanta daga igiyoyin aurensa.

Rikicin Sadiya Haruna da G-Fresh dai ya bazu a kafofin sada zumunta inda ake ta tofa albarkacin baki musamman bayan hirarsu da Hadiza Gabon.

Hadiza Gabon ta tattauna da Sadiya

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

A yau mako daya kenan da Hadiza Gabon ta saki tattaunawa da Sayyada Sadiya inda ta bayyana dalilin rabuwarta da tsohon mijinta.

A nan ne ta bayyana irin dambarwar da ta shiga tsakaninsu har lamarin da ya kai ga rabuwarsu.

Ta fara da bayyana cewa, a farko yaronta ne kuma ko a mafarki bata taba tsammanin za ta taba aurensa ba.

Amma kaddara wacce ta riga fata ta hada su kuma haka suka yi aure wanda bai ko dade ba.

Duba bidiyon mijin da Sadiya za ta aura a kasa:

Auren Sadiya Haruna da G-Fresh ya mutu

A wani labari na daban, jita-jitar mutuwar auren Sayyada Sadiya Haruna ta fara ne tun watan Yulin shekarar 2023. Wata daya tak bayan da aka daura mata aurenta da G-Fresh Al'amin.

An fara batun mutuwar auren ne bayan da Sadiya ta cire dukkanin hotuna da bidiyoyinsu tare a kafar sada zumunta, wanda ya kyasta wutar jita-jitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.