An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai

An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai

- Wata kungiyar yaki da cin hanci da rashaw ta bankado wata babbar badakala

- Ta bayyana cewa, ta gano wasu kadarori da wasu tsoffin gwamnoni suka mallaka

- Ta kuma bada rahoton da ta hada ga shugaban EFCC don gudanar da bincike

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Human and Development Debelopment Agenda, (HEDA) ta bankado wasu kadarori da wasu fitattun 'yan siyasan Najeriya suka mallaka a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.

Rahoton, wanda kungiyar HEDA ta hada ita ce ta dauki nauyin shi, amma Farfesa Gbenga Oduntan na jami’ar Kent ne ya yi bincike tare da hada shi.

Ya bayyana cewa, wasu tsoffin gwamoni, ministoci da sanatoci sun mallaki wasu manyan kadarori 130 a Dubai da ake zargin sun mallakesu ne ta hanyar wawashe dukiya daga Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai

An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai
An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai Hoto: thenationonlineng.com
Asali: UGC

Kadarorin suna daga cikin sama da 800 da aka gano mallakar 'yan Najeriya a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa da suka hada da manyan hafsoshin tsaro da sojoji.

Sun kuma samu ne daga cin hanci da rashawa, kauracewa haraji na kasuwanci, haramtattun ayyuka da kungiyoyi da kamfanonin kasuwanci ke yi da kuma sakamakon da aka samu daga ayyukan laifi.

Ko da yake rahoton bai bayyana ainihin 'yan siyasan da suka mallaki kadarorin a Dubai ba, Shugaban HEDA, Olanrewaju Suraj, wanda ya yi magana da jaridar The Nation ta wayar tarho a daren jiya, ya ce:

“Mun bar wa EFCC don warware badakalar. Abin takaici ne matuka cewa ana wawure kudadenmu ana boye su a kasashen waje.

"Ba ma kawai maganar kadarori a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa da aka gano mallakar wasu hafsoshin soja ba.”

Yayin karbar rahoton, shugaban hukumar ta EFCC, Bawa, ya ce: “Ina so na tabbatar muku cewa za mu yi nazarin rahoton domin mu kara darajar wadancan wuraren da yake cikin aikin mu; za mu dube shi kuma mu tabbatar da cewa an yi adalci.

“An dade ana cutar kasar nan, mutanen da aka dora masu nauyin gudanar da mulki a kasar nan sun yi nasarar yin hakan saboda son kai ta hanyar wawashe wadannan kudade daga kasar nan zuwa waje.

Ya ba da tabbacin dakatar da irin wannan badakalar anan gaba tare da tabbatar da dawo da dukiyoyin kasa Najeriya.

KU KARANTA: Sheikh Gumi da Obasanjo sun shawarci gwamnati da ta kirkiri kotun 'yan bindiga

A wani labarin, Mataimakiya ga shugaban kasar Najeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yakar cin hanci da rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafukan sada zumunta.

Ms Onochie ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter ranar Litinin, tana mai cewa za a gayyaci irin wadanan mutane domin bincike kan yaddaa suka mallaki kadarori da arzikin da suke shelantawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.